✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za a samu ci gaba a kasar nan ba sai da gudunmawar mata – Hajiya Halima

Hajiya Halima Amadu Jabiru, gogaggiyar ’yar siyasa ce da ta dade a siyasar Jihar Nasarawa da kasa baki daya. Ta fito takarar kujerun siyasa da…

Hajiya Halima Amadu Jabiru, gogaggiyar ’yar siyasa ce da ta dade a siyasar Jihar Nasarawa da kasa baki daya. Ta fito takarar kujerun siyasa da dama a jihar. A yanzu ita ce Kwamishiniyar Ma’aikatar Filaye da Tsare-Tsare a Jihar Nasarawa. A tattaunawarta da wakilinmu ta bayyana tarihin rayuwarta inda ta kuma kalubalanci mata su shiga harkar siyasa a dama da su don a cewarta ba zai yiwu a samu ci gaba a jihar da kasa baki daya ba tare da gudumawarsu ba. Ga yadda hirar ta kasance:

 

Tarihin rayuwata:

Sunana Hajiya Halima Amadu Jabiru. Ni ’yar asalin garin Lafiya ne a nan Jihar Nasarawa. Amma an haife ni ne a garin Lakwaja a 1967 a lokacin yana Jihar Kwara wanda yanzu shi ne hedikwatar Jihar Kogi. Na fara karatun firamare a Holy Trinity Transfer School kafin aiki ya koma da mahaifina Jihar Kwara inda na ci gaba da karatun firamare a St. Barnabas Primary School. Daga nan sai bayan wani lokaci aiki ya sake daga mahaifina zuwa jiharmu ta Nasarawa inda na kammala karatun sakandare a Gobernment Girls Secondary School da ke garin Garaku, Karamar Hukumar Garaku. Daga nan na ci gaba da karatu a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Jihar Filato da ke Jos inda na samu difloma  a fannin harkokin kudi (accounting). Da na kammala ne sai na ci gaba da karatu a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda na yi digiri. Na kuma ci gaba da karatu a Jami’ar ta Abubakar Tafawa Balewa, inda na yi karatu Babbar Diploma (Post graduate) duk a fannin harkokin kudi. Ni uwa ce kuma a yanzu ni daliba ce ina ci gaba da karatuna a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi inda nake digiri na biyu a fannin Kimiyyar Siyasa. Kuma a kwanakin baya Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura ya nada ni Kwamishinar Ma’aikatar Filaye da Tsare-Tsare.

Ayyuka:

Na fara aiki ne da bankin Lion Bank wanda ya koma Diamond Bank. Kasancewata uwa sai na fuskanci aikin banki yana takura min ta yadda ba na samun isasshen lokaci ga iyalina, hakan ya sa na bar aikin.

Daga nan na dawo ina aiki da kamfanin mai gidana da ake kira Lafiya Engineering Company inda na yi aiki a matsayin akanta. Na yi kimanin shekara 10 ina aiki da kamfanin. Ina aikin ina kuma taba siyasa daga bisani na shiga siyasa dumu-dumu. Kuma ina daya daga cikin wadanda suka fara kafa Jam’iyyar PDP a jihar nan a tsakanin 1998 zuwa 1999 inda muka yi ta gwargwarmaya a siyasance har Allah Ya kaddara na fito takarar kujerar mazabar Lafiya ta Tsakiya a Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa a shekarar 2003. Sai dai Allah bai kaddara na yi nasara ba. Duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba na sake neman kujerar a 2011 na kuma sake nema a 2015.

Kuma duka wadannan zabubbuka da na fito babu wanda ban samu ba. Sai dai saboda wasu dalilai da mu mata mukan samu kanmu ciki inda kullum ake ganin bai dace mace ta jagoranci al’umma ba. Shi ya sa za ka yi mamaki a dukan zabubbukan za ka ga da kuri’a kwaya biyu ne kacal ake wuce ni. A wani lokaci ma ka ji wai kwaya daya ce kacal. Zan iya tunawa ma a daya daga cikin zabubbukan akwai wanda da farko aka bayyana cewa mun yi kunnen doki da abokin karawata. Amma maimakon a maimaita zaben, sai aka bayyana shi cewa shi ya lashe zaben kuma hakan ya faru ne bayan an bayyana cewa ba a kirga wasu kuri’una ba wai don sun lalace. To amma a matsayina ta Musulma wace ta yarda da Allah da kuma kaddara ban kauce wa jam’iyyata ba. Na ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ina yi mata aiki don a kullum na tabbata cewa idan lokaci da Allah Ya ce za ka yi abu za ka yi.

Daga bisani ne na yanke shawarar canja sheka zuwa Jam’iyyar APC bayan na lura an samu ci gaba a fannonin rayuwa daban-daban a karkashin jagorancinta. Sai na ce dama ina fitowa neman kujerun siyasar ne saboda in ba da tawa gudunmawa ga ci gabar jihar nan, me zai sa ba zan shigo APC a yi tafiyar da ni ba? Domin a gaskiya akwai kamantawa da nuna gaskiya a wannan gwamnati ta Umaru Tanko Al-Makura. Amma kafin nan kamar yadda ka sani na yi aiki da Gwamnatin PDP da ta shude ta marigayi Gwamna Aliyu Akwai Doma, Allah Ya jikansa. Na yi aiki a lokacin a matsayin mai taimaka masa ta musamman da kuma mai ba shi shawara ta musamman da sauransu.

Abin da na koya daga iyayena:

Alhamdullillah na fito ne daga babban gida. Abin da nake nufi da babban gida shi ne na fito ne daga gidan sarauta inda za ka tarar da muhimman mutane. A bangaren iyayena mu ’yan sarauta ne. Iyayena ne ke rike da sarautar garin nan na Lafiya. Marigayi Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Isah Mustapha Agwai da ya rasu kwanan nan mahaifi ne a wajena. Don kakan mahaifiyata ya yi Sarki a Lafiya wato ya fito ne daga gidan sarautar Unguwar Galadimawa, wadanda a yanzu suke cewa su ma a sa su a jerin masu sarautar Lafiya wato gidan Sarautar Bage ke nan da ke Unguwar Galadimawa. Haka a bangaren mahaifina kakansa shi ne mai shari’ar gargajiya a lokacin. Duk shari’ar garin nan shi ne yake yi. Saboda haka na taso ne a gidan sarauta babba kuma hatta mai gidana shi ma dan sarki ne domin iyayensa sun yi sarauta a garin nan. Kuma duk wanda ya taso daga babban gida dole ne ya koyi kyakkyawar tarbiyya musamman na girmama na gaba da sanin muhimmancin mutum dan uwansa. Mun tashi mun san abin da ya dace, da abin da bai dace ba. Ba kamar abin da ke faruwa yanzu ba. A lokacinmu iyayenmu ma ba ruwansu da mu don makwabci zai iya hukunta mu idan muka aikata ba daidai ba, sai dai iyayenmu su ji labari su kuma yaba wa wanda ya hukunta ka. Amma yanzu idan ka kuskura ka taba dan wani ka ja wa kanka babban tashin hankali. Saboda haka a takaice na koyi tarbiyya mai kyau a wurin iyayena.

Nasarori da na cimma a rayuwata:

Allah Ya halicce ni mace ce da ba ta da tsoro. Duk abin da na tunkara a rayuwata ba na tsoro sai na kammala shi. Zan daraja ka in kuma girmama ka amma ba na tsoronka. Shi ya sa nakan fito in tsaya wa al’ummata musamman marasa galihu in bi musu hakkinsu. Dukan wadannan kujerun siyasa da na bayyana cewa na nema duk ina yi ne don in bauta wa al’ummata. Kuma a kullum ina tare da su. Shi ya sa da ka shigo nan ofishina ka ga jama’a da dama. Ina iya kokarina a kullun in tallafa musu iya gwargwado don na tabbata hakan shi ne babban dalilin kasancewarmu a duniyar nan. Saboda haka a takaice zan ce wannan shi ne babban nasara daga cikin dinbin nasarori da na cim ma a rayuwata da yardar Allah. Wato taimaka wa al’umma a koyaushe a kowane hali.

Yadda nake gudanar da harkokin gidana da aikin gwamnati:

Wato da farko na gode Allah don na fara siyasa ce bayan ’ya’yana sun girma sun mallaki hankalinsu. Kuma ni mace ce da a koyaushe nake tsara ayyukana ta yadda ba sa shafar harkokin gidana. A matsayin uwa ba na barin aikina ya shafi yadda nake kula da iyalina. Don a matsayina na Musulma hakki ne da ya rataya a wuyana in yi duk mai yiwuwa wajen kula da gidana yadda addinin Musulunci ya tanada. Shi ya sa shi kansa mai gidana Allah Ya jikansa ya yi ta yaba mini a wannan bangare kuma ya rika karfafa mini gwiwa ya kuma ba ni cikakken goyon baya. Yakan ce min na san za ki iya, na san ke wace ce. Duk abin da namiji zai yi don karfafa wa matarsa, wannan bawan Allah ya yi mini. Kada ka yi mamaki shi ya sa min kwadayin shiga siyasa. Akwai lokacin da muka tafi Umara a Saudiyya inda daga nan muka tafi yawo a wata kasa, sai wata rana ya kira ni ta waya ya ce ba za ki dawo gida ba? Ga Jam’iyyar PDP ta bude rajistar mambobinta. Ina zuwa gida Najeriya sai ya ce maza ki je ki yi rajista a yi da ke a PDP don na san za ki iya harkar. Wallahi yadda na fara ke nan. A duk lokacin da muka fita yawo da shi muna dawowa gida sai ya ce min kin manta kina da taron siyasa karfe kaza? Maza ki tafi ki  canja kaya ki tafi kada ki makara.

Kalubale da na fuskanta a rayuwa:

Babban kalubalen shi ne yadda ba a karfafa ko ba a bai wa mata damar da ta kamata don su ma su fito neman kujerun siyasa a jihar nan da kasa baki Daya kasancewa a yanzu siyasa ta koma sai da kuDi. Ya kamata a rika yin tsari ta yadda ba mata kawai ba duk wanda ya cancanta ya fito takarar kowace kujerar siyasa a kasar nan a ba shi damar ko yana da kuDi ko ba ya da shi. Na tabbata ta haka ne al’umma za su iya zabar shugabanni nagari. Kalubale na biyu kuma shi ne yadda waDansu maza ke Daukar mata cewa ba za su iya jagorancin al’umma a siyasance ba. Koda yake ba na ganin haka a matsayin kalubale shi ya sa duk da na sha wuya sosai a gwargwamayar siyasa da nake yi, amma duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba na ci gaba kuma ina koyon abubuwa da dama ta harkar don ina so ne in kasance a bar koyi da misali ga sauran ’yan uwana mata da ke tasowa.

Shawarata ga mata da matasa:

Shawarar ita ce kamar kullum bai kamata a ce ana harkokin siyasa da mulki da sauransu ba tare da mu mata ba. Idan ba a yi da mu mata, ta yaya za a san matsalolinmu. Kuma ba zai yiwu a samu ci gaba a kasar nan ba tare da gudunmawar mu mata ba. Kuma mata mu ne muke da yawan kuri’a da hakan ya ba mu damar fito da duk wanda muke so ya shugabance mu. Saboda haka dole ne mu fito kwanmu da kwarkwata mu zabi duk ’yan takararmu na Jam’iyyar APC daga sama har kasa a zabubbukan da ke tafe don ci gaba da gudanar da shugabancin jihar nan da kasa baki Daya da za su ci gaba da samar mana da romon dimokuraDiyya.

Kasashen waje da nake tafiya hutu:

A gaskiya kasancewata Musulma na fi tafiya aikin ibada ne a kasar Saudiyya. A duk lokaci da na samu hutu nakan ziyarci kasar don in gudanar da ibada ga Mahalicina in gode maSa a kan abubuwa da dama da Ya yi wa iyalina da ni kaina a rayuwata. Sauran kasashe da nake sha’awar tafiya kuma sun haDa da Faransa da Dubai da Landan da Amsterdam da sauransu. Amma na fi tafiya kasashe biyu wato Saudiyya da Dubai. Sauran kasashen da na bayyana auyuka ne suke kai ni.

Tufafin da na fi sha’awa:

Idan ka lura irin yadda waDansu mata ke fita irin ta Turawa ka ga suna sauye fatar jikinsu da sauransu ba ya burge ni. Ina son tufafi ne irin namu na matan Arewa. Don ni ’yar Arewa ce, uwa kuma Musulma. Dole ne in rika sa tufafin da za su tsare min mutunci a koyaushe kamar yadda addinin Musulunci ya tsara.