✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba yi zaɓen ƙananan hukumomi a Kaduna ba — PDP

Jami'yyar ta bayyana cewar hukumar ta gaza raba muhimman kayan aiki a jihar.

Jam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar Kaduna ta bayyana cewar ba a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar ba.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa zaɓen ya gudana ne kawai a wani yanki na Tudun Wada da ke Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu da misalin ƙarfe 3:30 na rana.

Amma, a wata tattaunawa ta wayar tarho, jami’ar hulɗa da jama’a ta PDP, Maria Dogo, ta ce ba a yi zaɓe a Kaduna ba.

Ta bayyana cewa, “An kai kayan zaɓe ofisoshin ƙananan hukumomi ba tare da sanar da wakilan jam’iyyu ba, kuma ba a haɗa takardun sakamako a cikin kayan ba.

“Wannan ba abin da za mu karɓa ba ne, kuma muna so mu sanar da jama’a cewa ba a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a Kaduna ba.”

A halin da ake ciki, Shugabar Hukumar Zaɓe ta Jihar Kaduna (KAD-SIECOM), Hajiya Hajara Mohammed, ta tabbatar wa jama’a cewa ba za a yi maguɗi a zaɓen ba.

Ta kuma gargadi ’yan siyasa da su guji tayar da tarzoma ko amfani da kalaman ƙiyayya, tare da kira ga jam’iyyun siyasa su tallafa wa hukumar wajen gudanar da zaɓen cikin lumana.

’Yan takarar ciyaman guda 79 daga jam’iyyu 10, waɗanda suka haɗa da APGA, APC, PDP, NNPP, PRP, LP, YPP, ADC, ZLP, da AA, ne suka shiga zaɓen.