✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba wanda zai yi rabin abin da Messi da Ronaldo suka yi a kwallo – Maradona

Tsohon Kyaftin din Argentina Diego Armando Maradona, ya ce Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun yi wa sauran ’yan wasa zarra, kuma ba ya tsammanin…

Tsohon Kyaftin din Argentina Diego Armando Maradona, ya ce Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun yi wa sauran ’yan wasa zarra, kuma ba ya tsammanin akwai wani dan wasan da zai yi rabin abin da suka yi a wasan tamola.

Shi kansa Maradona ana masa kallon daya daga cikin manyan ’yan wasan da aka taba samu a fagen kwallon kafa a duniya, bayan ya taka rawar gani, inda ya lashe kofuna a kungiyoyin kwallon kafa na Barcelona da Napoli, sannan ya lashe Kofin Duniya a 1986 lokacin da ya jagorancin kasarsa Argentina ta lashe kofin a kasar Mexico.

’Yan wasa kalilan ne suka zo kusa da Maradona a fagen taka leda, sai dai Messi da Ronaldo sun bi sahun ’yan wasan da za a ce duniyar kwallon kafa na alfahari da su.

Maradona mai shekaru 60 a duniya, a ranar Talatar da gabata ce Likitansa, Leopoldo Luque, ya bayyana cewa yana samun waraka bayan tiyata da aka yi masa a cikin kwakwalwa.

Diego wanda tun a shekarar 2019 yake a matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta Gimnasia da ke Argenitina, a baya-bayan nan ya yi ta fama da rashin lafiya ta kwanciyar jini a tsakanin fatar ta kai da kuma kwakwalwa.