✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba wanda zai bunkasa Kudancin Kaduna sai mutanen yankin  – Sarkin Fadan Kagoma

Sarkin Fadan Kagoma, Kanar Paul Zakka Wyom (mai ritaya), ya yi kira ga dukkan kabilun Kudancin Kaduna su hada kansu waje daya domin samar da…

Sarkin Fadan Kagoma, Kanar Paul Zakka Wyom (mai ritaya), ya yi kira ga dukkan kabilun Kudancin Kaduna su hada kansu waje daya domin samar da bikin Kalankuwa na bai-daya da za su rika gudanarwa.

Sarkin,  ya bayyana haka ne a wajen Bikin Gargajiya na Shekara-Shekara na Kabilar Gwong (Kagoma) da aka shirya a Fadan Kagoma da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, inda ya yi kira ga jama’ar yankin su daina jiran wani daga nesa ya zo don taimaka musu, maimakon haka, su yi amfani da arzikin da ke yankin musamman na citta wanda aka yi amanna tana daga cikin mafiya kyau a duniya.

Kanar Paul Zakka ya kuma yi kira ga jama’ar yankin su mara wa Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufa’i baya domin a cewarsa, da yawa daga cikin kyawawan manufofinsa sai nan gaba ne za a ga fa’idarsu.

A karshe Sarkin ya ce dole ne sai al’ummar Jihar Kaduna sun yi watsi da bambance-bambancen addini da na kabila tare da rungumar kowa da kowa don samun ci gaba da kuma daukaka jihar baki daya.

Babban Bako Mai Jawabi,  kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Dokta Obadiah Mailafia ya bayyana tasirin al’adun kasashen ketare musamman na Yammacin Turai a matsayin daya daga cikin dalilan gurbacewar tarbiyyar matasa a wannan zamani, musamman ta fuskar shaye-shayen miyagun kwayoyi da yin watsi da kyawawan tadoji da aka gada iyaye da kakanni.

Dokta Mailafia, wanda ya yi bayani kan yadda za a yi amfani da bukukuwan gargajiya wajen samar da hadin kai da musayar al’adu, tare da bunkasa tattalin arziki da tsaron kasa, ya koka kan yawan hare-haren da ake kaiwa a garuruwan Kudancin Kaduna, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ya ce lokaci ya yi da kowane mutum zai yi amfani da damar da yake da ita da kuma abin da Allah Ya ba shi don bayar da gudunmawarsa wajen bunkasa tattalin arzikin Kudancin Kaduna ta hanyar tallafawa da kawo abubuwan ci gaba da suka hada da masana’antu da kamfanoni da manyan makarantu masu zaman kansu, inda ya bada misali da Dokajen Jaba, Cif Anthony Hassan, wanda a yanzu haka yake gina jami’a mai zaman kanta a garin Kachiya.

Shugaban Karamar Hukumar Jama’a Mista Danjuma Peter Aberik, ya ce ci gaba kowane iri na samuwa ne kawai idan jama’a sun rungumi juna ta hanyar zaman lafiya da mutunta juna wanda shi ne tsanin kaiwa ga kowane irin ci gaba.

Sannan ya yaba wa mutanen masarautar kan yadda suka rike al’adunsu da kyau, inda ya shawarce su da su kara bunkasa al’adunsu ta hanyar amfani da hanyoyin sadarwar fasahar zamani don saukaka wa duk wani mai sha’awar dubawa ko yin nazari a ko’ina yake a fadin duniya.