A wata ganawa da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi da Fira-Ministar Birtaniya, Theresa May, ya bayyana cewa bai damu da takarar 2019 ba, domin hankalinsa na kan abin da ya shafi magance matsalar rashin tsaro ne da kuma tattalin arziki.
Shugabannin biyu dai sun yi wannan tattaunawa ce a wata ganawa da suka yi, a Gidan Gwamnatin Birtaniya da ke lamba 10 kan Titin Downing, a Birnin Landan ranar Litinin da ya gabata.
“Kafin mu hau mulki mun gina yakin neman zabenmu a kan muhimman abubuwa uku; samar da tsaro a kasa; farfado da tattalin arzki da kuma yaki da cin hanci da rashawa. To akwai zabe kuma dake tafe cikin shekara mai zuwa, tuni har ‘yan siyasa sun maida hankulansu akan zaben, amma dai ni ban damu ba, na fi damuwa da tsaro da tattalin arziki.”
Buhari ya ci gaba da cewa Najeriya da Birtaniya sun dade da cimma hadin kai a tsakaninsu ta fannoni da dama. “Ya kamata mutane su san yadda suka kawo a matsayin da suke a yanzu, idan har su na so su ci gaba. Amma sai aka tafka kuskure a baya-bayan nan har aka daina koyar da darasin tarihi a makarantunmu. Amma gwamnatinmu kuma a yanzu za mu maido shi a cikin manhajar darussan da ake koyarwa a makarantu.”
Shugaba Buhari ya kuma yaba wa wasu kamfanonin Birtaniya irin su Cadbury, Unileber da wasu da dama, wadanda ya ce, “sun jajirce a Najeriya duk rintsin wahalhalu da matsaloli, tun kafin Yakin Basasa, ta inda har a lokacin yakin ma ba su kwashe kayansu sun fice daga Najeriya ba.
“Amma duk da haka mu na bukatar karin wasu masu zuba jarin daga nan Birtaniya, domin su shigo Najeriya. Muna kuma godiya dangane da goyon bayan da ku ke bayarwa na kayan aiki da kuma bayar da horo ga jami’an sojojinmu, musamman a lokacin da muke yaki da Boko Haram. Amma mu na so mu ci gaba da hulda da ku a fannin kasuwanci da zuba jari.”
Haka kuma Shugaba Buhari ya kuma bayyana wa Fira-Ministar kokarin ci gaban da aka samu a Najeriya a fannnin noma, inda ya furta cewa a yanzu mun rage shigo da shinkafa ya zuwa kashi 90 bisa 100, ta yadda a yanzu Najeriya ce ke ciyar da kan ta daga cikin gida ba sai an dogara da shigo da abinci daga waje ba.