✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba ni da niyyar yi wa matata kishiya – Tinubu

Ya ce sam ba shi da niyyar yi wa Oluremi kishiya

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya karyata labarin da ake yadawa cewa ya shirya tsaf domin yi wa matarsa kishiya.

Ya bayyana labarin, wanda ake ta yadawa a kafafen sada zumunta a matsayin na kanzon kurege, inda ya ce matarsa daya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ishe shi.

Mai magana da yawun dan takarar, Tunde Rahman ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi.

Ya ce, “Mun ga wani labari da yake ta yawo a kafafen sada zumunta cewa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, zai kara aure.

“Wannan labari ne na kanzon kurege, kuma wanda ba shi da tushe. Mai girma Tinubu na jin dadin aurensa da Sanata Oluremi Tinubu, wanda Allah Ya albarkata da ’ya’ya na gari, kuma ba shi da aniyar kara auren wata matar yanzu, ko Musulma ce ko kuma Kirista.

“Masu yada wannan labarin cewa zai auri Musulma suna yin haka ne ba wai don kawai su kawo rudani a cikin iyalinsa ba ne, suna kuma so ne su jefa kiyayyarsa a zukatan Kiristoci, kuma ba za su je ko ina ba,” in ji sanarwar.

Daga nan sai ya bukaci daukacin ’yan Najeriya da su yi watsi da labarin, inda ya ce yanzu babban burin dan takarar shi ne babban zabe mai zuwa da yadda zai inganta rayuwar ’yan Najeriya, ba wai kara aure ba.