✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da kudin sayen littattafai, harkokina sun tsaya cak – Sheik Abduljabbar

Ya ce tun da aka tsare shi a gidan gyaran hali harkokinsa suka tsaya cak.

Malamin addinin Musuluncin nan da Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar a gaban kotu kan zargin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W), Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara, ya ce a yanzu ba shi da kudin sayen littattafai sakamakon tsayawar harkokinsa cak, tun lokacin da aka tsare shi a kurkuku.

Ya bayyana hakan ne a gaban kotun Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano ranar Alhamis, yayin da aka dawo ci gaba da sauraron kararsa.

Yana magana ne lokacin da kotun ta umarce shi da ya sayi litattafan Hadisan Sahihu Muslim da Sahihul Bukhari wadanda ba su da sharhi ko fassara a ciki, kamar yadda ya bukaci a bashi su, inda shi kuma ya shaida wa kotun cewa ba shi da kudin saye.

“Ba ni da kudin da zan iya sayen litattafan hadisan nan guda biyu saboda tunda aka tsare ni a gidan gyaran hali tsawon watanni biyar, harkokina suka tsaya cak,” inji shi.

Anan ne Daraktar Shigar da Kara ta Gwamnatin Jihar kano Barista Aisha Mahmood, ta dauki alkawarin cewa Gwamnatin Kano za ta ba wanda ake kara kudin da zai sayi litattafan kafin nan da ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamban 2021.

Kotun ta ce za a saya masa littattafan ne domin ya sami damar yin tambayoyi ga shaidar da bangaren masu kara suka gabatar a gaban kotun.

Idan za a iya tunawa, Gwamantin Jihar Kano ce ta yi karar malamin gaban kotun bisa tuhumarsa da laifukan yin batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Tun da farko,  lauyoyin da ke gabatar da kara karkashin jagorancin Farfesa Mamman Lawan Yusufari (SAN), sun sake gabatar wa kotu shaidarsu na biyu, mai suna Murtala Kabir Muhammad  wanda mazaunin unguwar Kofar Na’isa, Lokon Makera ne, wanda kuma dalibin Malam Abduljabbar ne, domin ya amsa tambayoyi.

Sai dai lokacin da aka ba wanda ake kara damar yin tambayoyi ga shaida na biyu,  sai ya fara yin amfani da wani littafi, inda yake budawa yana karanta tambayoyi ga shaidar.

Hakan ya sa lauyoyin masu kara suka yi suka akai, inda suka ce littafin da Abduljabbar din yake amfani da shi wajen yin tambayoyi ba shi ne wanda shaidarsu ya ce ya duba ba.

A cewarsu, “Shaidarmu ya bayyana cewa littafin Sahihu Muslim da Sahihul Bukhari da ya duba a matsayin manazarta da wanda ake kara ya gaya wa dalibansa a lokacin da ya yi wadancan kalamai na batanci da ake zargin sa da yi ga Annabi Muhammad (SAW) ba masu sharhi ba ne, irin wanda Abduljabbar ke amfani da shi a gaban kotun.”

Har ila yau, masu gabatar da karar sun roki kotu da ta nemi mai kula da dakin karatu na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ya kawo wa kotun litattafan Hadisan biyu, ba wai a matsayin shaida ba, amma a matsayin abin da zai taimaka wa kotu wajen gudanar da shari’ar.

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ta amince da rokon masu gabatar da kara, inda ta umarci Magatakardar kotun da ya rubuta takarda ga dakin karatun Jami’ar don kawo wa kotun wadannan littattafan.

Kotun ta dage shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamban 2021 don ci gaba da shari’ar.

Sai dai tunda farko a zaman kotun sai da kotun ta fara warware kwarya-kwaryar hukuncin da ta yi a zamanta na ranar 28 ga watan Oktoban 2021.

A lokacin dai kotun ta yanke cewa wanda ake kara tare da shi da layoyinsa ba za su hadu a lokaci guda don kare shi ba sai dai ya zabi daya; ko ya kare kansa da kansa ko kuma ya bar lauyoyinsa su kare shi.

A yanzu dai kotun ta bayyana amincewarta cewa wanda ake kara ya yi wa shaida tambayoyi da kansa haka kuma lauyoyinsa za su ci gaba da kare shi a cikin shari’ar dogaro da sashe na 36 (a) na Kundin Tsarin Mulkin  Kasar Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yi wa gyara.