✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Ba na nadamar shan guba saboda Maryam Yahaya’

Wanda ya sha guba saboda rashin ganin jarumar ya sake yin tafiyayya ko zai yi dace

Wani matashi da ya yi yunkurin kashe kansa a kwanakin baya ta hanyar shan fiya-fiya saboda ya gaza yin tozali da ‘yar fim din Hausa Maryam Yahaya ya sake dawowa Kano domin cika burinsa.

A hirarsa da Aminiya a ranar Asabar, matashin mai suna Musa Abdullahi ya ce yana nan a kan bakarsa na ganin jarumar kuma ba ya nadamar shan gubar da ya yi saboda ita.

“Nadamata guda daya ce ta rashin ganinta a kwanakin baya, amma ba ta shan fiya-fiya ba”, inji Musa mai shekaru 21.

Musa kenan a lokacin da ya sha gubar kwanakin baya.

To sai dai ya koka cewa wadanda suka ba shi masauki a zuwansa na farko yanzu sun ki yarda su sauke shi saboda tsoron kada a koma gidan jiya.

‘Laifin matashin ne’

Shugaban Kungiyar Jaruman Kannywood Reshen Jihar Kano, Alhassan Kwalle, ya dora laifin gazawar matashin ya ga Maryam tun da farko a kan rashin sanar da ita kafin zuwansa.

Alhassan ya ce jarumar ba ta san matashin ba ballantana batun zuwansa, in ban da sanin ta da ya yi a cikin shirin fim.

Ya ce duba da halin da ake ciki na rashin tsaro, ba zai yiwu ta gana da shi ba tare da ta san shi ko ta san da zuwansa ba.

Da Aminiya ta tuntubi Musa a kan ko ya sanar da jarumar a wannan karon kafin ya taho sai ya ce a’a, amma yana da kwarin gwiwar cewa a wannan karon hakarsa za ta cimma ruwa.

Wace ce Maryam Yahaya?

Maryam Yahaya daya ce daga cikin matasan jarumai a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood wadanda tauraruwarsu ke haskawa.

‘Yar kimanin shekaru 23, Maryam ta fara tashe ne bayan fitowarta a wani fim mai suna ‘Mansoor’ wanda Ali Nuhu ya ba da umarni.

Haifaffiyar unguwar Goron Dutse da ke Kano, jarumar ta yi karatunta na firamare a unguwar Yelwa, sai sakandare a Makarantar ‘Ya’yan Sojoji da ke Barikin Bukavu a Kano.

Daga baya ta samu shiga masana’antar Kannywood, abun da ta dade tana burin yi.

Ta fara fita ne a wani fim mai suna ‘Gidan Abinci’ a matsayin karamar jaruma kafin daga bisani tauraruwarta ta haska bayan rawar da ta taka a fim din Mansoor.