✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba na nadama da sana’ar fim – Rabi’u Rikadawa

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Rabi’u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila ya bayyana cewa ba ya nadamar yin sana’ar fim saboda alheran da suke…

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Rabi’u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila ya bayyana cewa ba ya nadamar yin sana’ar fim saboda alheran da suke cikinta ba su da iyaka.
Ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan rediyon Faransa a makon jiya.
Jarumin ya kuma bayyana irin gudunmawar da suke bayarwa ta hanyar wayar da kan al’umma a matsayin ladan sai dai Allah Ya biya su, amma ba wai kudin da ake sayen fim ya isa ya biya su jajircewar da suke yi wajen fadakar da al’umma ba.
“Ka san Bahaushe ya ce ana kaunar wawa ba a kaunar haihuwarsa. Mu wadansu irin al’umma ne da suka soyu ga jama’a, sannan wani lokaci kuma jama’ar nan daga cikinsu suke nuna mana kiyayya, ina za su gan ka su buge, wadansu kuma suna nuna mana soyayya, matanmu suna hakuri domin ko ba ma nan za ka ga an je har gidajenmu, su karbe su, idan muna nan kuma mu karbe su, wani lokaci akwai masu zuwa don su ga matar wane, kuna gida za ku ji wata ta yi sallama ta ce wai za ta kewaya, ba hakan ne ya kawo ta ba, so take ta ga yaya matar wane take. Sai bayan ta fito sai ka ji ta ce ke ce matar wane ko? Daga nan su zauna su yi hira, ka ga duk kauna ce, kaunar da ake mana ce ta gangaro har ta shafi iyalinmu.
“Wani lokaci daga wani abu ya faru sai ka ga an fara yi mana yayyafin zagi, wannan al’amari ba ya daga mini hankali, saboda rashin fahimta ce ta haifar da hakan, duk da wannan dambarwar da ake tafkawa, to ina alfahari da sana’ar fim, ina kuma godiya ga Allahu (SWT) da Ya zabar mini sana’ar fim. Sana’ar fim tana da albarka, ba ya ga sayar da fuskarka da kake yi ka ci tuwo, babu wurin da za ka je neman wata alfarma ba ka samu ba, sai wani babban mutum mai mukami ya je neman alfarma yana bin hanya, ya kuma dade, amma kana zuwa masu ba da abin daga nesa za su hango ka sai su taso, ga Dila can, wannan ba Rikadawa ba ne? Ga Daushe nan, su ne za su taso su ce maka ranka ya dade barka da zuwa, da zarar ka ce musu abu kaza kake so, sai su ce zo a yi maka. Ina so in nuna maka albarka ta wannan sana’a, yau idan wani wanda ba ya wannan sana’a ya rasu iyakacin ’yan uwansa da abokansa ne za su sani, su kadai ne za su yi masa addu’a, amma mu idan muka rasu duniya ce take yi mana addu’a. Duniya ce take cewa Allah Ya jikan wane. Ka ga wannan ma ba karamin abu ne ba. Idan na fada maka alheran da suke cikin harkar fim ni wurina ba su da iyaka,” inji shi.
Ya ce babban abin da ya sa yake alfahari da sana’ar fim shi ne wayar da kan jama’a da harkar ke yi, inda ’yan fim ke ba da gudunmawa wajen fadakar da al’umma.
Ya ce: “Idan ba zan manta ba tun zamanin da Turawa suka tafi suka bar mu, idan har ana neman a wayar da kan al’umma kan wani abu da ya shige musu duhu, walau fannin noma ko lafiya, hatta irin takin zamanin nan lokacin da ya shigo ana so a yi amfani da su, da masu wasannin kwaikwayo da makada da mawaka aka yi amfani wajen nusar da jama’a ga yadda ake amfani da shi. Ban mantawa lokacin da kiliya ta koma dama, da masu wasannin kwaikwayo aka yi amfani, a nan mutane suka fahimci kiliya fa ta koma dama, a yanzu da muke tafiya har Allah Ya kawo mu wannan lokaci, idan ka kula ko a fannin siyasa, sannan idan tashe-tashen hankula sun faru mu din ake nema don mu fadakar da jama’a sakon zaman lafiya ya fi zama dan sarki; tashin hankali ba shi da amfani da sauransu. Ba ya ga nishadantarwa da ke biyo baya, tabbas muna ba da muhimmiyar gudunmuwa ta fannin wayar da kan kan al’umma.”
A karshe Rikadawa ya bukaci gwamnati ta rika taimaka wa masu sana’ar wadanda suka tsufa kamar su Audu Karkuzu da Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja, saboda irin gudunmuwar da suka bayar wajen wayar da kan al’umma.