Majalisar Wakilai ta ce ba ta aminta da tsawaita wa’adin amfani da tsohuwar Naira da karin kwanaki 10 da Babban Bankin Najeriya CBN ya yi ba.
Kwamitin Majalisar mai ruwa da tsaki kan sha’anin sauya fasalin wasu takardun Naira, ya ce dole CBN ya yi abin da ya kamata kamar yadda yake kunshe a sassa na 20 da 3 da 4 da kuma 5 na Dokar Babban Bankin Kasar.
“Tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da kwana 10 ba shi ne mafita ba.
“A matsayinmu na Kwamitin Majalisa ba za mu amince da wani abu sabanin abin da sassa na 20 da 3 da 4 da kuma 5 na Dokar CBN suka nuna ba,” in ji shugaban kwamitin, Honorabul Alhassan Ado Doguwa.
Da fari dai CBN ya kayyade 31 ga Janairu a matsayin lokacin da za a daina karbar tsoffin takardun N200 da N500 da kuma N1000.
Sai dai kuma a wannan Lahadin, an ambato Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da izinin tsaiwata wa’adin zuwa 10 ga Fabrairu.
A martaninsa dangane da tsawaita wa’adin, kwamitin ta bakin shugabansa Honorabul Alhassan Ado Doguwa, ya ce bai yarda da karin ba.
Ya ce dole CBN ya koma ya yi biyayya ga tanade-tanden da ke kunshe a sassa na 20 da 3 da 4 da kuma 5 na Dokar CBN.
A cewar Doguwa, “Najeriya kasa ce mai tasowa don haka wajibi ne a kiyaye tsare-tsaren da doka ta shimfida.
“Muna ganin akwai wasu take-take da wannan tsari na sauya takardun naira na yi wa Babban Zaben da ke tafe zagon kasa.
“Sanin kowa ne cewa ta hanyar fitar da tsabar kudade ake biyan alawus-alawus din jami’an tsaro da ke jibintar lamarin gudanar da zabe a kasar nan musamman a matakin jiha.
“Kuma Majalisar za ta rattaba hannu kan izinin kamo Gwamnan CBN don tilasta masa bayyana a gabanta,” in ji shi.
Idan ba a manta ba, a zamanta na Talatar da ta gabata, Majalisar ta kafa kwamitin biyo bayan korafe-korafen ‘yan kasa kan matakin canjin kudi da CBN ya dauka.