✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Ba mu yafe wa ’yan Boko Haram da suka mika wuya ba’

’Yan gudun hijira sun ki yafewa, sarakuna sun nemi a hukunta su, sojoji sun sa musu ido.

’Yan gudun hijira sun ce ba za su yafe wa mayaka da kwamandojin kungiyar Boko Haram da suka mika wuya, irin asarar da da suka ja musu ba.

A zantawarmu da su bayan mayaka da kwamandojin kungiyar sama da 1,000 sun suka mika wuya ga sojojin Najeriya, suna kuma neman a yafe musu abin da suka yi a baya, ’yan gudun hijirar sun ce da wuya su iya zama tare da mutanen da suka yi musu barnar da ba za ta misaltu ba.

Wasu dattawan Arewa da sarakuna na zargin tubar muzuru mayakan suka yi.

A cewarsu, kamata ya yi a gurfanar da tubabbun ’yan kungiyar su fuskanci hukunci kan abin da suka aikata, a yayin da kwararru ke yin kashedi da cewa ba girin-girin ba, ta yi mai.

‘Gwamnati ba ta kyauta ba’

Wani dan gudun hijira daga Guzamala, Ali Mohammed, da muka zanta da shi game da mika wuyan ’yan Boko Haram din ya ce shekara bakwai ke nan yana zaman gudun hijira bayan ya baro kauyensu kuma har yanzu ba a iya zama a kauyen nasu.

Ya kuma yi watsi da afuwar da za a yi wa ’yan Boko Haram din da ya ce sun mayar da su mabarata, marasa matsuguni.

“Da wuya ka iya yafe wa dan ta’adda,” inji shi.

“Muna ta jin wani bakon labari wai ’yan Boko Haram da suka tuba ko suka mika wuya za su dawo cikin al’umma.

“In dai haka ne to gwamnati ba ta damu abin da ya same mu ba, abu mai sauki ne a furta cewa a yafe, amma wadannan miyagun mutanen sun bata mana rayuwa, kuma sai a ce za a karbe su a cikin al’umma kamar wasu gwaraza? Ai gwamnati ba ta yi mana adalci ba.” inji Ali.

Da kamar wuya…

Ita ma wata matashi ’yar gudun mai suna Salma, ta ce tana mamakin yadda mutane za su iya zama da tsoffin ’yan Boko Haram din a cikinsu.

“Ni matashiya ce amma an riga an lalata min rayuwa, ba ni kadai ba har da iyalaina, kuma rayuwarmu ba za ta taba dawowa daidai ba.

“Ina ganin gara kawai gwamnati ta gina musu wani gari su kadai ta ajiye su,” inji ta.

Wani mazuanin Maiduguri, Abdullahi Saidu ya ce mutane ba za su zauna da tsoffin ’yan Boko Haram ba kuma ba za su yarda su zauna a cikinsu ba.

“Mutanen nan da ke riya cewa sun tuba, su suka kashe mana abokai da abokan kasuwanci; wadansu daga cikinsu har iyayensu suka kashe da kansu.

“Ta yaya za ka yi tsammanin mu zauna da su alhali su ne suka daidaita mana rayuwa da kuma kasarmu?”

Wata mahaifiya mai suna Bintu Mala, wadda ta ce ’yan Boko Haram sun kashe dan uwanta a 2014, ta ce wasu ’yan Boko Haram din da suka mika wuya ba da gaske suke yi ba, saboda haka bai kamata a dawo da su cikin jama’a ba.

“Wasunsu sun mika wuya ne saboda abokan hamayyarsu sun kashe musu shugabanni, wadansu kuma saboda sojoji sun tarwatsa maboyarsu; Mutanen nan na iya komawa daji ko ma bayar da bayanai,”

’Yan Boko Haram ne suka mika wuya

Wasu mutane dai na shakku a kan mika wuya ga sojojin Najeriya da wasu mayaka da kwamandojin kungiyar sama da 1,000 suka yi a baya-bayan nan a Jihar Borno.

Mayakan da kwamandojin kungiyar, ciki har da manyan masu hada musu bama-bamai sun mika wuya ne bayan sojoji sun ritsa su na tsawon lokaci a maboyansu da ke Dajin Sambisa da yankunan da ke makwabtaka da Dutsen Mandara a Jihar Borno.

Aminiya ta gano ’yan tsirarun mayakan kungiyar da suka ci gaba da yaki gwamnati al’ummomi, dakarun gwamnati sun murkushe su, ba su da zabi face su mika wuya, su karbi ‘afuwar’ da gwamnati da yi, ko kuma su sha dalma.

Mun tuntubi Daraktan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Olufemi Sawyer, game da shakkun da wasu suke da shi, cewa mutanen da suka mika wuya ba ’yan Boko Haram ba ne.

Manjo-Janar Sawyer ya yi watsi da zargin, sannan yi kira da cewa ’yan Najeriya zu guyi neman kawo rudani.

A cewarsa, idan wadanda suka mika wuya ba ’yan Boko Haram ba ne, to ta yaya aka gano da ’yan matan Chibok din da ’yan kungiyar suka aura tsawon shekara bakwai a cikin iyalan wadanda da suka mika wuyan.

Sun saba yaudara —Basarake

Hakimin Chibok, Injiniya Zanna Modu Chibok, ya ce fitowar wadanda suka mika wuya a Karamar Hukumar Mafa ba tare da makamansu ba na iya zama wata yaudara ce.

“Gaskiya akwai abin damuwa, duk da cewa abu ne mai kyau a ce ’yan Boko Haram sun mika wuya, amma sai an yi hattara saboda a baya an yi irin haka.

“Ba a dade ba sai muka gane cewa sun sake komawa cikin daji, saboda haka sai mun lura sosai.

“Ni dai ban natsu ba cewa sun tuba da gaske; ina ganin akwai abin da suka shirya, shi ya sa suka mika wuya, amma akwai alamar tambaya kan yadda suka fito ba tare da makamansu ba.

“Ni na fi ganin a hukunta duk ’yan Boko Haram din da suka kashe wa mutane iyaye, suka sace ’ya’ya suka yi musu auren dole; Duk wanda ya aikata laifin yaki, kamata ya yi a kai shi kotu.

“Addini ya koyar da mu yin yafiya, amma a irin wannan yanayi abu ne mai wuya, domin Allah ne Ya kiyaye amma da sun shafe mu a ban kasa.

“Ni dai shawarata ita ce gwamnati ta samu wani wuri ta ajiye su na tsaon lokaci inda kwata-kwata wadanda suka yi wa laifi ba za su gan su ba,” inji basaraken.

Abin da ya sa su mika wuya

Janar Sawyer ya ce dokar yaki ta duniya ce ta sa sojoji suka karbe su, saboa “Akwai doka, idan har mayaka suka mika wuya…Ba za a kashe su ba.”

Wasu majiyoyi masu kusanci da rundunar da ke yaki da Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabas ta ce wasu daga cikin mutanen da suka yi ta fitowa daga maboyar Boko Haram suka mika wuya ’yan Boko Haram ne, kuma tubar su ta gaskiya ce, sun kuma amince a yi musu duk abin da ya kamata na sauya tunaninsu domin su dawo cikin al’umma su ci gaba da rayuwa.

Amma sun ce sai masu kula da sha’annin tsaro a Arewa Maso Gabas da ke karbar ‘tubabbun’ ’yan Boko Haram din sun yi taka-tsantsan, saboda wasu mayakan za su iya yaudara, domin yaki dan yaudara ne.

Mika wuya ba ta taba ISWAP ba

Aminya ta gano cewa babu ’yan bangaren ISWAP a cikin mayaka da kwamandojojin da suka mika wuya ga sojoji.

Wadanda suka mika wuyan mutane ne da aka tilasta musu shiga kungiyar tare da matansa da ’ya’yansu su sama da 1,000 a yankunan Bama da Gwoza da Mafa da Konduga da sauransu a yakin Kudanci da Tsakiyar Jihar Borno.

Yawancin mutanen da ke da sansani a Dajin Sambisa da Dutsen Mandara, mazauna wuraren ne tun kafin bullar Boko Haram.

Bayan bullar kungiyar ta yi wa wasu daga cikinsu romon baka ko ta tursasa musu shiga cikinta, shi ya sa suke futowa bayan abubuwa sun sauya.

Sun tuba ko sun mika wuya ne bayan mutuwar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, wanda ya kashe kansa bayan ’yan ISWAP sun ritsa shi a maboyarsa a Dajin Sambisa.

’Yan ISWAP wadanda bangare ne na kungiyar ISIS, sun so Shekau da mataimakansa su yi musu mubaya’a.

Ana cikin turkaturkar, Shekau ya matsa maballin rigar kunar bakin wakensa, ya kashe kansa da wasu manyan kwamandojojin kungiyarsa da ’yan ISWAP da ke wurin tattaunawar.

Mutuwar ta Shekau ta girgiza wasu daga cikin kanana da matsakaitan kwamandojoji da mayakan Boko Haram, kamar yadda muka samu bayani.

Tun kafin mutuwarsa, Shekau ya yi alkawarin ba zai taba mika wuya ba ga ISWAP, wadda Abu Musab Al-Barnawy, dan Shugaban Boko Haram na farko kuma wanda ya kafa ta Mohammed Yusuf, yake jagoranta.

Bayan mutuwar Shekau, mayakan ISWAP sun rika bin magoya bayansa da ke a kan bakarsa na kin yin mubaya’a gare su suna ragargazar su.

Majiyarmu ta sanar da mu cewa bayan mutuwar Shekau mayakansa ba su da kwakkwaran jagoranci ballantana su iya tunkarar ISWAP.

Rashin karfin fada da sojoji da kuma matsa musu da ISWAP ta yi ya wargaza su, shi ya sa wadanda aka tursasa wa shiga kungiyar da wadanda suka gaji da yaki suka yi ta tururuwar mika wuya ga sojoji.

An kuma gano cewa wasu daga cikinsu sun “amince” sun koma ISWAP sauran kuma suka mika wuya ga sojojin Najeriya.

– Bayan mika wuya: ISWAP ta bautar da yaran Shekau

“Amma ISWAP ta mayar da wandanda suka mika mata wuya kaskantattu a hannunta.

“Wasu kwamandojin tawaga a karkashin Shekau yanzu sun sama ’yan kalla a karkashin ISWAP.

“Har wadanda a lokacin Shekau gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi da alkalai da limamai ne a yankunan da kungiyar ke cin karen ta babu babbaka — yanzu ba su da ta cewa.

“An kwace makamansu an kuma rage musu matsayi, wasu ma an tsare saboda sun nemi nuna wa sabbin iyayen gidansu tsaurin kai.

“Shi ya sa wasunsu da suka ga za su yi batan bakatantan suka gwammace su mika wuya ga sojojin Najeriya…Abin da ke faruwa ke nan.

“Wasu mayakan sun mika wuya ne saboda ba su da zabi; Shekau bai raini wanda zai gaje shi ba; Shi da kanshi ya sha kashe mataimakansa da ya kamata su gaje shi ko da ya mutu,” inji majiyarmu.

Wa’adin ISWAP ya sa su mika wuya

Aminiya ta gano cewa gabanin mika wuya da magoya bayan na Shekau suka yi ga sojoji, ISWAP ta ba su wa’adi cewa su yi mata mubaya’a su shigo cikinta ko kuma su san inda dare ya yi musu.

Wa’adin zai kare nan da mako biyu masu zuwa, daga nan kuma mayakan ISWAP za su yi musu dirar mikiya.

Wani tsohon hafsan soji, Salihu Bakhari, ya ce, “Yawancin wadanda suka fito din kauyawa ne. An samu gabala a kan mayakan Shekau da suka rage.

“Amma dole a nemo amsar wasu muhimman tambayoyi: Idan har ’yan Boko Haram din ne, me ya sa suke fitowa babu makamai? Ina kayan soji da sauran kayan yakin da muke ganin su a ciki?

“Ya kamata masu kula da sake tsugunar da su su bayyana wa jama’a wadannan abubuwa domin mutane su samu nutsuwa.

“Sannan gwamnati ta sa ido saboda ’yan ISWAP na nan yadda suke, dauke da makamansu suna jiran damina ta wuce su ci gaba da addabar mutane,” inji shi.

Sannan sojoji kar su rudu da wannan nasarar da suke ganin sun samu domin “mayakan ISWAP sun watsu a wurare da dama a yankin Tabkin Chadi; Mu je har can mu yake su mu gani ko za mu iya sa su mu su mika wuya.

“Amm su ’yan Boko Haram da Shekau yake jagoranta sun karaya ne tun bayan rasuwarsa,” inji shi.

Shi ma wani tsohon hafsan soji da ke da kusanci da yaki da ta’addanci, ya ce, “Idan aka lura da wuraren da suke fitowa, mabiyan Shakau ne, ba sa jin dadin yadda ISWAP ta kawo musu rabuwar kai.

“ISWAP ta bar mayakanta suna daukar makamansu amma ta hana ’yan Boko Haram; an dai yarda su rika taruwa amma an takaita zirga-zirgarsu kuma ba a yarda su yi amfani da wayoyi ba,” inji shi.

Abin da ya kamata

Game da yadda za a yi da wadanda suka tuban, ya ce “abu ne mai sauki idan har gwamnati za ta samar da kyakkyawan yanayin da ya dace bayan an gama yi musu horo.

“Kar gwamnati ta yi musu alkawarin da ta san ba za ta cika ba; Yanzu haka wadanda aka gama horaswa a Gombe ba a ba su kayan sana’a ba.

“Kashi 80 cikin 100 na wadanda suke fitowa ’yan asalin wuraren ne, saboda haka sake tsugunar da su ba abu ne mai wuya ba.

“Duk da haka dole sai gwamnanti ta bunkasa bangaren sauya tunanin mutane da tubabbun mayakan domin kauce wa irin abin da ya faru lokacin da ’yan Gwoza da aka dawo da su daga cibiyar horaswa da ke Gombe, aka ajiye su a sansanin ’yan gudun hijirar Bakassi da ke kan hanyar Damboa a Maiduguri.

“’Yan gudun hijirar da ke sansanin sun yi bore, dole aka sauya wa tubabbun ’yan ta’addan wuri daga nan din,” inji shi.

Babbar dama —Kareto

Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, Mohammed Kareto, ya ce an shekara kusan 12 ana yaki da Boko Haram, yanzu dama ta samu na kawo karshen lamarin.

“Mayakan Boko Haram sama da 1,000 ne aka ce sun mika wuya a kwanan nan.

“Hakan ya yi kyau saboda ya nuna sun gaji da yaki, an ci garfinsu kuma da alama akwai baraka a shugabancinsu, watakila saboda hankoron masu neman shugabanci bayan mutuwar Shekau.

“A bayyane yake cewa sojoji sun karfafa matakan soji da na farar hula a yaki da ta’addanci.

“Amma kar su yi hanzarin mayar da tubabbun ’yan ta’addan cikin al’umma domin da wuya mutane su karbe su.

“Ba bakon abu ba ne bangare daya (’yan Boko Haram din) su hakura da abin da zai biyo baya, amma dai kar a yi saurin shigar da su cikin mutane.

“Ya kamata a dauki bayanansu yadda ya kamata, a san wadanda aka tursasa musu zama ’yan Boko Haram, kamar ’yan matan Chibok da ire-irensu, da wadanda da kansu suka shiga kungiyar,” inji shi.

Sai an yi sa sarakuna —Farfesa Gudunbali

Wani Farfesan Kimiyyar Siyasa a Jam’iar Maiduguri, Umara Ibrahim Gudumbali ya bukaci a shigar da sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da kuma sojoji a cikin shirin sauya tunanin tsoffin mayakan Boko Haram da kuma shigar da su cikin al’umma.

“Sauya tunanin tsohon dan ta’adda batu ne na tunani da zuyica da kuma akidar da mutum ya ginu a kanda wadda ta kauce daga akidar sauran mutane.

“Idan ana so sauya akidar mutum, to akwai bayanan da ake bukatar a sani game da shi, misali, daga ina kowannensu ya fito? Shin gwamnati ta bar sarakunan gargajiya sun tabbatar cewa ’yan Boko Haram ne ko kuma mutanen gari? Ba a ba wa mutane wadannan bayanai sun tantance ba.”