Wadansu daga cikin ’yan gudun hijirar da suke sansanonin gudun hijira na Maiduguri sun yi zargin cewa ba su taba samun tallafin abincin da gwamnati ko kungiyoyin sa kai suke bayarwa ba, a sansanonin ’yan gudun hijira sama da 10 da ake da su ba a birnin.
daya daga cikin ’yan gudun hijirar, Malam Musa Da’u, wanda ya fito daga karamar Hukumar Gwoza kuma yake zaune a sansanin Bakasi, ya ce, “A gaskiya ban taba samun abincin da gwamnati ko kungiyoyi masu zaman kansu suke rabawa a wannan sansani ba, kuma ire-irena mun kai sama da 300, muna wuni mu kwana da yunwa. Duk da yawan iyalanmu sai dai mu fita mu yi aikin kwadago ko itace mu sayar mu sayo abinci, sai dai in ga abinci a wurin wadansu. Ga ni kuma da mata biyu da ’ya’ya takwas. Ban dora wa kowa laifi ba domin ba rabona ba ne.”
Malama Falmata Ali, wadda ta fito daga Kukawa kuma take sansanin Gidajen Malamai na Pompamari, ta ce, “Abincin da gwamnati ke rabawa sai dai in gani a gidan wadansu domin har yanzu bai kawo gare ni ba, gani da ’ya’ya marayu biyar, sai dai in makwabtanmu sun ci sun rage su ba ni. Haka muke wuni ko kwana da yunwa, kuma ba ni kadai ba ce na san akalla ’yan gudun hijira sama da 100 da ba su samun abincin. Ko saboda ba mu san hanyoyin da ake bi a samu ba ne ko kuma babu rabonmu ne ba sani ba. To amma ina rokon gwamnati ta tausaya mana ta sa mu a cikin wadanda ake ba su abincin don ceto rayuwarmu.”
Wani an gudun hijirar mai suna Audu Aliyu, da ke sansanin Dalori One, wanda ya fito daga karamar Hukumar Bama, ya ce “Akwai ’yan gudun hijirar da ba su samun abincin da hukumomi suke rabawa kuma ba mu san dalili ba. Ga shi ina da mata 2 da ’ya’ya 6, a kullum sai na shiga gari na yi aikin kwadago sannan zan samu abin da za mu ci. Duk yadda za a yi a samu wannan tallafi na yi iyakacin kokarina amma abin ya ci tura.”
Sai dai Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Injiniya Ahmed Satomi ya shaida wa wakilinmu cewa, kowane dan gudun hijira yana karbar abinci isasshe da zai kai shi tsawon wata guda shi da iyalansa, babu mutum daya da ba a ba shi abinci a sansanonin a iya saninsa.
“Ana bai wa kowane mutum da iyalinsa nau’o’in abinci a tsarin da muka bullo da shi na mutum da iyalinsa, kuma ana ba su babban buhun shinkafa da katan din taliya da semobita da bura-bisko da sauran kayan abinci. Saboda haka a iya sanina babu mutum daya da ba a ba shi abinci a duk sansanonin da muke da su a garin nan. In kuma akwai, to ina kalubalantarsa ya fito ya bayyana kansa da hujjoji gamsassu, ina tabbatar maka idan gaskiya ce za a ba shi tare da ba shi hakuri kan akasin da aka samu.”