Gwamnatin tarayya ta ce alhakin bayyana inda likitocin nan ‘yan China da suka zo Najeriya don taimakawa a yaki annobar coronavirus ba a wuyanta yake ba, tun da ba ita ba ce ta gayyace su.
An dai yi ta takaddama a kan zuwan likitocin wadanda suka iso Najeriya ranar 8 ga watan Afrilu sannan suka killace kansu na tsawon kwanaki 14, daga bisani aka yi masu gwaji aka tabbatar da duk ba sa dauke da kwayar cutar coronavirus.
Nazarin da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta yi a kan su a wani waje da ba a bayyana ba ya nuna ba sa dauke da cutar .
Ministan Lafiya Osagie Ehaire ya ce likitocin ba bakin gwamnatin Najeriya ba ne, ma’aikatan kamfanin gine-gine ne na China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC).
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Abuja lokacin da yake bayani ga manema labarai a zaman kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don hana yaduwar cutar COVID-19 karo na 31.
“Ina tunanin ba duka ayarin ba ne likitoci, na samu labarin wasu daga cikinsu injiniyoyi ne, amma dai ma’aikatan kamfanin CCECC ne.
“Ba ma’aikatar lafiya ba ce ta sauke su, don haka ba za mu iya yin bayani game da su ba ko kuma a wanne hali suke ciki.
“Na ga alama hankalin mutane yana kan wadannan likitocin. Sai dai su ma’aikatan kamfani ne kuma sun iso kasar nan ne ta hanyar bizar kamfani.
“Zan yi matukar farin ciki idan ba ku tambaye ni inda suke ba, saboda ba bakinmu ba ne”, inji Dokta Ehanire.
Ministan ya kara da cewa, likitocin ba su zo don su kula da masu jinyar COVID-19 a Najeriya ba.