Kungiyar Ma’aikata ta Najeriya (TUC) ta ce ba ta samu wani umarnin kotu da ya hana ta shiga yajin aikin da ta fara ba.
Shugaban kungiyar, Festus Osifo ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Laraba.
Gwamnatin Tarayya da Ministan Shari’a, sun shigar da karar neman kotu ta hana kungiyoyin tsunduma yajin aiki.
A hukuncin da ya yanke, Shugaban Kotun Masana’antu na Kasa, Mai Shari’a Benedict Kanyip, ya ba da umarnin dakatar da kungiyoyin daga shiga yajin aiki.
Osifo ya ce bai kamata kungiyoyin NLC da TUC su ki bin umarnin kotun ba.
Kungiyoin kwadago a Najeriya (NLC da TUC) sun umarci maboninsu kungiyoyin ma’aikata da ke karkashin inuwarsu da su da tsunduma yajin aiki a fadin kasar nan daga tsakar daren ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023.
Yajin aikin dai ya fara kamari kuma yana rana ta biyu, lamarin da ya janyo cikas ga ayyukan ma’aikata da dama da fadin kasar nan.