Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta mayar da martani kan rahotannin da ke zargin cewa ta kai samame gidan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa da EFCC ta fitar a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun kakakinta, Wilson Uwujaren, ta yi watsi da labarin tare da bayyana cewar ba ta kai samame gidan dan takarar ba.
- NAJERIYA A YAU: Shin don talakawa gwamnoni ke adawa da canjin kudi?
- Tsohon Shugaban PDP a Kano ya sauya sheka zuwa NNPP
Ta kuma bayyana cewa ba ta kwato makudan kudi kimanin Naira biliyan 400 a gidan Tinubu ba kamar yadda aka yada.
“An ja hankalin EFCC, kan wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa jami’an hukumar sun kai samame gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, a zabe mai zuwa cewar an kwato makudan kudi har Naira biliyan 400.
“Hukumar tana so ta bayyana cewa babu wani samame da EFCC ta kai. An bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton saboda ba gaskiya ba ne.”
Tun da fari dai an yada labarin a kafafen sada zumunta cewar hukumar ta gano wasu makudan kudade a gidan tsohon gwamnan na Jihar Legas.