Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ce za ta ci gaba da gudanar da yajin aikin da ta fara kan neman karin mafi karancin albashi.
NLC ta ce yajin aikin zai ci gaba sai idan ta zauna da sauran bangarorinta sun amince da sassautawa ko janye shi.
A safiyar Talata kungiyar ta sanar da haka bayan da farko ta cimma matsaya da bangaren gwamnati cewa Shugaba Tinubu za ta kara mafi karancin albashin daga Naira 60,000 daku kungiyar ta ki amincewa.
Ana iya tuna cewa kungiyar ta kekashe kasa cewa N494,000 ne za ta amince da shi a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.
- Karin albashi: Nan gaba za mu sanar da matsayarmu kan yajin aiki —NLC
- NAJERIYA A YAU: Yadda Yajin Aiki Ke Durkusar Da Sana’o’i
A yayin zaman na ranar Litinin, bangarorin sun amince cewa gwamnati za ta kara kudin daga N60,000 sannan za su ci gaba da tattaunawa a kullum na tsawon mako guda domin cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashin.
Sun kuma amince cewa kungiyar za ta isar da tayin da gwamnati ta yi ga sauran bangarorinta domin cimma matsaya domin janye yajin aijin, sannan ba za a cutar da duk wani ma’aikaci da ya shiga yajin aikin ba.
A safiyar Talata da kungiyar za ta yi nata zaman ne kuma ta sanar cewa yajin aikin da ta fara yana nan daram, har sai idan bangarorin nata sun sauya shawara.
Tuni dai yajin aikin ya gurgunta harkokin tattalin arziki da ma sauran sha’anin yau da kullum a Najeriya.
Kasuwanni, bankuna, makarantu da cibiyoyin gwamnati da kamfanoni sun sun kasance a rufe a sakamakon yajin aikin.
A ranar Litinin da aka fara yajin aikin, kungiyar kare hakkin al’ummar Musulmi, MURIC, ta koka bisa yadda lamarin ya kawo tsaiko ga jigilar maniyyata aikin Hajji zuwa kasar Saudiyya.
MURIC ta nuna damuwa cewa wani jirgi ya zo daukar maniyyata, amma haka ya koma Saudiyya ba tare ya dauki maniyyatan ba a sakamakon yajin aikin.
Sanarwar kungiyar ta nuna damuwa bisa yadda dubban maniyyata suka makale a sansanonin alhazai bayan sun baro iyalansu da nufin tafiya don sauke farali.
Amma a wata sanarwar da Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta fitar, ta ba da tabbacin cewa yajin aikin ba zai hana kammala jigilar maniyyatan da suka rage zuwa Saudiyya ba.
Sanarwar da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara, ta ba da tabbacin kammala jigilar maniyyatan kafin ko a ranar 10 ga watan nan na Yuni, kamar yadda aka tsara.
A halin da ake ciki aka fara jigilar maniyyatan Jihar Jigawa a ranar Litinin.