✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba mu da wani shafin Hausa in ba na Aminiya ba – Daily Trust

Shafin da kawai Daily Trust ke da shi na Hausa shi ne Aminiya

Kamfanin jarida na Daily Trust ya nesanta kansa daga wani shafi a dandalin Facebook mai suna ‘Daily Trust Hausa’ da ma wasu da ke yin sojan gona da sunansa suna yada labaran karya.

Kamfanin ya ce ya lura cewa akwai shafuka da dama da aka bude a dandalin sada zumunta na Facebook, da suke yin sojan gona wajen yin amfani da sunansa, ko alamarsa, don kawai su yaudari jama’a a matsayin su ne.

Wasu daga cikin irin wadannan shafukan ba su tsaya a iya yada labarun da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, ko ma na karya, wasu har kyaututtuka suke rabawa da sunanmu.

Aminiya na daya daga cikin gidajen jaridun da kamfanin gamayyar kafafen yada labarai na Media Trust ya mallaka, wanda kuma shi yake da sabon gidan talabijin na Trust TV.

Yayin da wasu daga cikin wadannan shafukan ke amfani da sunanmu (Aminiya) kai tsaye, wasu kuma na kara ‘Hausa’ a gaban sunan jaridar mu ta Turanci, su kira kansu da Daily Trust Hausa, ko wani sunan makamancin haka.

Sai dai duk kokarinmu na kai korafin irin wadannan shafukan ga dandalin Facebook don daukar matakan da suka dace, alamu na nuni da cewa har yanzu ya ki yin abin da ya dace.

Saboda haka, ya zama wajibi mu bayyana cewa shafin Hausa da Kamfanin Media Trust yake da shi kawai shi ne na Aminiya wanda ke da alamar tantancewar Facebook mai launin shudi da kuma masu bibiyar harkokinsa kusan 700,00 da kuma wadanda suke tare da shi sama da 360,000.

Dandalin Facebook da sauran jama’a su lura cewa duk wani shafi da yake amfani da kowane daya daga cikin sunayen da muka bayyana a sama, ba namu ba ne, kuma ba ruwanmu da ko me suke wallafawa a cikinsu.

Ga hotunan wasu daga cikin irin wadannan shafukan na bogi a kasa.