Ƙungiyar Jakadun Zaman Lafiya ta Jihar Kano, sun ce ba su da hannu a ƙone-ƙone da fasa shagunan mutane da aka yi, yayin zanga-zangar yunwa da aka yi a jihar a ranar Alhamis.
Shugaban Kungiyar, Nasiru Usman Naibawa ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Asabar.
- Zanga-zanga: Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi
- Zanga-zanga: Mutum 2 sun mutu a arangamar ’yan daba da jami’an tsaro a Kano
Naibawa, wanda tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso ne a jihar, ya ce sun gudanar da gangamin lumana daga ofishinsu da ke Audu Bako Way don gabatar da wasiƙa ga Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero a ƙaramar fada da ke Nassarawa.
Ya ce sun yi niyyar gabatar da irin wannan wasiƙa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf, amma suka fasa sakamakon shawarar hukumomin tsaro a jihar.
A cewar Naibawa, shugaba Bola Tinubu yana buƙatar ƙarin lokaci kafin shawo kan ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.
Ya yi kira ga masu kishin ƙasa da su daina shiga zanga-zangar da ke gudana wadda ta kai ga karya doka da oda.
Naibawa ya ƙara da cewa babu ɗaya daga cikin mutane sama da 300 da aka kama a jihar da ke da alaƙa da ƙungiyar.
Ya buƙaci Gwamnatin Jihar Kano, da ta daina siyasantar da lamarin tare da mayar da hankali kan harkokin mulki.