✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu da hannu a kone ofishin Sanata Barau —APC

Gandujiyya ta ce zargin ba wani abu ba ne illa yunkurin goga wa manyan mutane da gwamnati kashin kaji

Tsagin Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje na Jam’iyyar APC a jiyar ya musanta zargin da ake masa da hannu a harin da ’yan daba suka kai ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Ibrahim Jibrin.

Sanata Barau na tare da tsagin Sanata Shekarau da ke adawa da tsagin Ganduje, kuma a satin da ya gabata ne kotu ba wa tsagin nasu shugabancin jam’iyyar APC a jihar.

Da sanyin safiyar ranar Alhamis ne wasu ’yan daba dauke da muggan makamai suka farmaki ofishin yakin neman zaben gwamnan Sanata Barau, suka banka masa wuta.

A sakamakon haka, tsagin Sanata Shekarau ya shigar da kara ga Shugaban ’Yan Sandan Najeriya tare da zargin mabiya bangaren Ganduje da daukar nauyin harin.

Amma da yake mayar da martani a kan lamarin, kakakin APC tsagin Ganduje, Ahmed S. Aruwa, ya ce zargin ba shi da tushe, kuma wani yunkuri ne na bata suna manyan mutane da kuma jam’iyyar.

Kazalika, ya ce wadansu da ake zargi suna da hannu a harin sun dauki lokaci ba sa Najeriya ballantana a yi tunanin suna da hannu a lamarin.

Aruwa, ya kara da cewa magoya bayan Ganduje mutane ne masu bin doka da oda, kuma babu wani dalili da zai sai su sanya kansu cikin muggan ayyuka irin wannan.