Gwamnatin Tarayya ta amince cewa ta gaza cika alkwarin da ta kulla da kungiyar Malama Jami’o’i ta kasa a bara ba. Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana haka lokacin da yake bayani ga manema labarai na Fadar Shugaban kasa a shekaranjiya Laraba bayan kammala taron Majalisar Zartarwa a karkashin Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.
Ya ce, “Na tabbatar gwamnati ba ta cika alkawarin da ta dauka a bangrenta ba, kuma duk da ba mu jin dadin ASUU ta shiga yajin aiki ba tare da bi ka’ida ko ba mu sanarwar da dace ba, amma mun yarda mun yi wasu alkawura da ba mu cika ba.”
Malam Adamu, wanda ya ce zai gana da shugabannin kungiya a shekaranjiya ko jiya, ya ce yana da yakinin za a cimma wasu yarjejeniyoyi kuma a janye yajin aikin cikin gaggawa.
Sai dai Ministan ya nanata cewa gwamnati ba za ta amince da bukatar kungiyar na a cire jami’o’i daga asusun hadaka na TSA ba, inda ya ce, “Ina cikke da bakin cikin cewa ina nan amma ASUU suna yajin aiki. A bara mun gana saboda ASUU ta bayar da wa’adin mako don fara yajin aiki kuma muka samu nasarar kulla yarjejeniya. Akwai batun wasu alawus kuma ina jin saboda katsewar sadarwa abin da muka yi alkawari bai samu ba, ama ina tabbatar wa ASUU da daukacin kasar nan, za a yi hakan.”
Ministan ya kuma kaddamar da kwamitocin sake tattaunawa kan yarjejeniyar da aka cimma da kungiyoyin Kwalejojin Ilimi da na Kimiyya a shekarar 2010, inda ya ce ya kamata a sake duba yarjejeniyar tun shekarar 2013 amma hakan bai samu ba saboda wasu matsalolin da suka taso.
An nada Shugaban Hukumar Gudanawa ta Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Tarayya da ke Damaturu Alhaji Mohammed Abubakar ya jagoranci tattaunawa da kungiyoyin kwalejojin kimiyya, yayin da aka nada takwaransa na Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Obudu, Dokta Obi Anthony ya jagoranci tattaunawa da na kwalejojin ilimin. Kowane kwamiti yana da wakilai 14 da suka kunshi masu ruwa-da-tsaki da suka fito daga bangarori daban-daban.