✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba manhajar ilimi ba ce matsala – Farfesa Junaidu

Shugaban Hukumar Bincike da Bunkasa Ilimi ta kasa (NERDC), Farfesa Isma’il Junaidu, ya musanta zargin da wasu masana suka yi cewa manhajar ilimin da ake…

Shugaban Hukumar Bincike da Bunkasa Ilimi ta kasa (NERDC), Farfesa Isma’il Junaidu, ya musanta zargin da wasu masana suka yi cewa manhajar ilimin da ake amfani da ita a kasar nan ita ce babbar matsalar da ke jawo koma-baya a fannin ilimi.

Farfesan wanda ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja, ya bayyana cewa manhajar ilimin kasar nan tana da inganci da nagarta. “Manhajarmu tana da inganci da nagarta. Ita ce ma manhajar da ta fi kowace a nahiyar Afirka,” inji shi.
Ya bayyana cewa hatta hukumar da ke sa ido a kan ilimi ta kasa-da-kasa ta yaba wa Najeriya, inda ta bayyana manhajar kasar a matsayin wacce ta fi kowace nagarta a nahiyar Afirka.
Ya ce ba nan gizo ke saka ba sai dai ya nemi da a duba a ga shin malamai suna koyarwa kamar yadda ya kamata a makarantu ko kuwa ba sa koyarwa? Ya ce mutane na korafin cewa malamai ba su koyarwa saboda ba a biyansu albashi.
Ya bayyana cewa muddin idan aka ce malami ya yi shekara ba a biya shi albashi ba, babu yadda zai koyar da dalibai.
Daga nan sai ya bayyana takaicinsa dangane da yadda koyar da malamai yadda za su dabbaka manhajar ilimi ya zama wani babban kalubale.
Ya kara da cewa saboda haka ne ma hukumar NERDC ta bayar da horo ga malamai 40 wadanda daga bisani za su koma jihohinsu su koyar. Amma ya ce hakan bai tabbata a wasu jihohi ba saboda irin yadda aka yi wa lamarin rikon sakainar-kashi.
Ya ce akwai kalubale da dalilai da yawa da suka janyo dalibai suke faduwa a darussan Lissafi da Ingilishi. Kamar yadda ya bayyana, dalilan sun hada da rashin bin ka’idar manhajar ilimi da hukumar ta tsara da karancin malamai da rashin kayan aiki da kuma rashin kwararrun malamai.