’Yan gwagwarmaya, wato Kwamarawa sun koka kan abin da suka ce ana yi masu na cin fuska a shafukan sada zumunta a ’yan kwanakin nan.
Kalmar Kwamarawa, wacce jam’in Kwamared ce, ana yi wa ’yan gwagwarmayar dalibai a makaranta, a ’yan kwanakin suna shan zolaya da tsokana a kafafen sada zumuntar, musamman daga wajen ’yan mata.
- Tsananin kaunar Tinubu ta sa matashi yin tattaki daga Gombe zuwa Legas
- Zan iya kwada wa saurayina mari a kan ‘bestie’ — Budurwa
Ana dai zargin cewa yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), shi ne babban dalilin ingiza al’amari inda tun bayan tsundumarta yajin aikin, kwamarawa daga makarantu daban-daban suka koma zaman gida tare da iyayensu ba kamar yadda suka saba a makaranta ba.
A makarantu, an san Kwamared da gwagwarmaya da fadi tashin ci gaban walwalar dalibai ta kowacce fuska, wannan ya sa da yawansu suke a karkashin wata kungiyar ci gaba ko kuma walwalar dalibai.
Masu irin wadannan zolaya na ganin yanzu Kwamarawa na gida babu harkokin gwagwarmaya balle a samu na walwala kamar yadda aka saba, wannan ya tilasta su amfani da abin da suka samu a hannun iyayensu.
Wasu kuma na ganin Kwamarawa sune irin mutanen nan ’yan boko masu iya-yi da suke zaune babu sana’a ba aikin yi, sai kinibibi, sannan ba aure sai zaman gwauranta da fada da kanne a gida wajen rabon abinci.
A cikin irin zolayar da ake wa Kwamarawa akwai irinsu an samu labarin an rufe wa Kwamared kunun bude-baki da murfin buta a gida, wannan yasa tun daga lokacin Kwamared ya ki ci ya ki sha, sai zazzaga Turanci yake abinsa saboda bacin rai.
Wasu kuma kan ce idan mutum ya je neman aure iyayen amarya kan tambaya shin mutum yana da sana’a ko kuma shima Kwamared ne sai gwagwarmaya ya sa a gaba.
Ire-iren wadannan da ma wasu daban suka sanya Kwamarawa nuna rashin jin dadinsu kan abin da ake masu da bayyana cewa ba su cancanci irin wannan sakayyar ba.
Abba D Hussein, wanda shi ma Kwamared ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa “Kalmar Kwamared na nufin dan gwagwarmaya da Hausa, wanda ba tsoro a fuskarsa ballantana a zuciyarsa, wanda ya sadaukar da nishadinsa don walwalar alummarsa.”
Har wa yau, wani Hassan Saeed ya ce, “Mu Kwamarawa, abin da ake mana a social media ba ma jin dadinsa…yana mana tukuki a makwallatan zuciyarmu, duk irin gwagwarmayar da muke amma munzama abun zolaya”.