✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba lallai ta’addanci ya kare nan da shekaru 20 masu zuwa ba – Buratai

Ya ce ’yan ta’addan sun gurbata tunanin mutane tsawon lokaci, cin galaba a kansu zai yi wahala.

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ya ce ba lallai ne ta’addancin kungiyar Boko Haram ya kare a Najeriya nan da shekaru 20 masu zuwa ba.

Ya ce ’yan ta’addan sun gurbata tunanin mutane da dama tsawon lokaci, lamarin da zai sa cin galaba a kansu cikin kankanin lokaci ya yi wahala.

Buratai ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da ya bayyana gaba Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar Dattijai domin a tantance shi a matsayin jakadan Najeriya.

Ya ce duk da yake dakarun Najeriya da hadin gwiwar takwarorinsu na makwabtan kasashe sun sami gagarumar nasara a yakin, duk da haka ba lallai ne a ga bayan matsalar cikin kankanin lokaci ba.

Buratai ya ce akwai wasu batutuwan siyasa da zamntakewa da ya kamata a fara magancewa kafin a kawo karshen matsalar.

“Dakarunmu na aiki kafada da kafada da takwarorinsu na Chadi da Kamaru. Mun sami gagarumar nasara, amma su kuma ’yan ta’addan suna shiga cikin yankunanmu kane-kane.

“Jihata ta Borno ita ce cibiyar wannan rikici kuma akidunsu sun shiga cikin zukatan mutane ta yadda ba abu ne mai sauki cire shi ba.

“Sojoji kadai ba za su iya magance matsalar ba, dole sai an samarwa da al’umma kayan more rayuwa.

“Zan iya kirga Kananan Hukumomi kusan guda biyar a Borno wadanda ba su da hanya. Haka lamarin yake a Zamfara da Katsina da Sakkwato. A jihohin Arewa da dama akwai yankunan da har yanzu ba su ma san da gwamnati ba saboda rashin hanyoyi da sauran kayan more rayuwa.

“Ba lallai ne wannan rikicin ya kare nan da shekaru 20 masu zuwa. Mun yi kokari sosai, amma ba zai yuwu mu ci gaba da amfani da dabaru iri daya mu yi tsammanin samun sakamako na daban ba,” inji Buaratai.