Biyo bayan mayar da yajin aikin da take yi zuwa na sai abin da hali ya yi, Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ta ce akwai yiwuwar ba za ta kara zaman tattaunawa da gwamnati ba har wa’adin mulkin Shugaban Buhari ya kare.
Wani mamba daga kwamitin zartarwar kungiyar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yayin da zu su ci gaba da gudanar da yajin aikin sai baba-ta-ganin, sun rufe tattaunawa da gwamnati.
- Za a shafe kwana 4 ana tafka ruwan sama a Kaduna da Bauchi – NiMet
- Kashi 10 na masu shan miyagun kwayoyi a Najeriya ‘yan Kaduna ne – NDLEA
Sai dai da wakilinmu ya nemi karin haske kan wannan batu ya ki cewa komai.
Haka kuma ya ce gabanin fara tattaunawa a taron da kungiyar ta gudanar da ‘ya’yanta, an samu hayaniya, musamman kan batun da shugaban kungiyar Emmanuel Osodeke ya yi da ke nuna raini ga jami`un.
“Malamai da yawa daga jami’o’in ABU da BUK da FUD da na Kudancin Najeriya na ganin tattaunawar da ake yi da gwamnatin ba ta da wata fa’ida, don haka a dakatar har sai gwamnatin ta sauka a 2023.
“Ba wai ba mu da tausayi ba ne, don mu ma ya shafe mu, ko ni ina da ‘ya’ya a jami’o’in nan, kuma watansu shida a gida.
“Sannan tsawon watanni shidan nan ba na karbar albashi, amma hakan bai hana ni yin abin da ya dace ba domin ceto su daga lalacewa”, inji shi.
A hannu guda kuma Shugaban Kungiyar Dalibai na Kasa (NAN) Asefon Sunday, ya ce karin wa’adin yajin aikin ASUU saboda kin biyansu albashin wata shida son zuciya ne karara suka nuna.
“Kashi 85 na bukatun ASUU an samu matsaya a kansu, amma saboda son zuciya sun ki janye yajin aiki.
“Suna kuma yaudarar mutane da batun gyaran jami’o’i, amma yaki kan walwalarsu ya fi yawa a batun yaji aikin,” inji Shugaban na NANS.
Shi ma dai Kakakin Ma’aikatar Ilimi ta Kasa, Bem Ben Goong, ya ce ba hurumin ASUU ba ne dagewa sai gwamnati ta sauya tsare-tsarenta.
Ya ce aikin ASUU a dokance kamar sauran kungiyoyi shi ne kokarin samarwa ‘ya’yanta walwala, sai dai kaso 95 na bukatunta na 2009, ba kan haka ba ne.
Haka kuma ya yi Allah wadai da batun ASUU na cewa su ne sanadiyyar kawo ci gaban jami’o’in kawo wannan lokacin.