✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba dan gidan Marigayi Abacha na aura ba —Hafsat Idris

To wannan ba gaskiya ba ce don ba shi da alaka da su.

Fitacciyar ‘yar wasa a masana’antar Kannywood, Hafsat Idris ta ce ba dan gidan tsohon Shugaban Kasa Marigayi Sani Abacha ta aura ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa jarumar ta yi aure ne a ranar Asabar a asirce a Jihar Kano.

A yayin da ake ta shagali da murnar wannan aure, sai aka fara rade-radin cewa dan tsohon Shugaban Kasa Abacha ta aura.

Sai dai cewarta, “ina godiya ga dukan masoya ‘yan uwa da abokan arziki na fatan alheri da suka min.

“Sai dai ina so na yi magana a kan rade-radin da ke yawo musamman a Intanet cewa mijin da na aura yana da alaka da gidan Abacha.

“To wannan ba gaskiya ba ce. Ba shi da alaka da su. Na gode.”

Majiyarmu ta ce ana tunanin cewa mijin da ta aura yana da alaka da matar dan Abachan, Mohammad Sani Abacha.