✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba daidai ba ne Majalisa ta tafi hutu ana fama da matsalar tsaro — Falana

Ya ce ba lallai ne Majalisar ta shigu ba kafin lokacin

Lauyan nan mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana, ya caccaki Majalisar Dokoki ta Kasa kan tafiya hutu a daidai lokacin da ya ce Najeriya na fuskantar mummunan kalubalen tsaro.

A yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels ranar Alhamis, lauyan ya ce ’yan majalisar ba sa daukar matsalar da muhimmancin da ya kamata.

A ranar Laraba ce dai Majalisar Dokokin ta yanke shawarar tafiya hutun kusan mako takwas, inda za ta dawo ranar 20 ga watan Satumban 2022.

Amma a cewar Falana, “Su [’yan majalisar] za su tafi hutun mako takwas. Ba zai yiwu ka tafi hutu ba a lokacin da kasarka ke ci da wuta.

“Wa’adin mako shidan ma da Sanatoci suka ba Shugaban Kasa ya magance matsalar tsaro ba mai yiwuwa ba ne, kwana bakwai ya kamata su ba shi

“Dalili kuwa shi ne, ba lallai ne nan da sati shidan na Majalisar ta shigu ba. An rurrufe makarantu.

“Ko a jiya muna da bikin rantsar da sabbin lauyoyi, amma dole ta sa mun canza wajen, sannan aka bukaci iyaye da su kaucewa wajen saboda gudun abin da zai iya faruwa.

“Na yi tsammanin ’yan majalisar za su dauki wannan batun da muhimmanci, amma ba su yi ba,” inji Falana.