Kungiyar ’Yan Fansho ta Kasa (NUP) reshen jihar Gombe, ta nesanta kanta daga wata ziyara da wasu mambobinta suka kai wa dan takarar Gwamnan Jihar na jam’iyyar PDP a jihar Gombe.
Shugaban kungiyar a jihar, Muhammed Hassan Kwami, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Kara Dage Dawowar Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
- Tserarrun fursunoni sun yi garkuwa da lauya mace a Fatakwal
Ya ce kungiyarsu ba ta da wata alaka da ziyarar, kuma mambobin sun kai ziyarar ce ta kashin kansu ba tare da yawun kungiyar ko yardarsu, ba hasali ma ba su tuntube su ba.
A cewarsa, Gwamnatin Gombe, karkashin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya tana biyansu kudadensu na fansho a kai a kai, kuma duk wadanda suka yi ritaya daga aiki a jihar da Kananan Hukumomi suna shiga shirin fansho bayan wata daya da yin ritayarsu.
Ya kuma ce zuwa yanzu gwamnatin jihar ta Gombe ta taka muhimmiyar rawa sosai wajen rage basukan ’yan fansho a jihar.
Sannan Hassan Kwami, ya bukaci mambobin kungiyar da su dinga yaba kokarin gwamnati tare da yin hakuri da tallafa wa manufofin gwamnati da shirye-shiryenta a kowane lokaci.
Daga nan sai ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da tsayuwar Daka wajen ganin an kyautata rayuwar mambobin kungiyar a kowane lokaci.