Wadansu shugabannin al’umma da mutanen Zariya sun fara korafi kan yadda alkalai da jami’an shari’a suke sakin wadanda aka kama da zargin yin garkuwa da mutane wadanda wadansu ma har sun yanke musu hukunci dauri a kurukuku.
Sun ce hakan yana kawo koma-baya ga kokarin da hukumomi suke yi wajen yaki da ’yan ta’adatan da suke gallabar jama’a a kewayen birnin Zariya da Jihar Kaduna baki daya.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa sakamakon hare-haren ta’addanci da sace jama’a a kewaye birnin Zariya, mutane suna kara dimauta ganin yadda wadansu daga cikin ’yan ta’addan da jami’an tsaro suka kama ko jama’a suka kama suka mika musu ke dawowa suna yawonsu a gari, bayan ’yan kwanaki da kama su.
Dagacin Wusasa, Injiniya Isiyaku Danlami Yusufu, wadda ya ce ba a wasa ko shiririta da lamarin da ya shafi tsaro a wannan lokaci, ya ce sakin wadanda aka kama da kin aiwatar musu da hukunci yana ruguza harkar tsaro, kuma yana ruruta fitina ko sa wasu daukar doka a hannu.
Ya ce, Gundumar Wusasa tana kan gaba wajen fama da rashin tsaro, wanda a cewarsa bai rasa nasaba da sakin wadanda aka kama da satar mutane da hukumomin shari’a ke yi, inda ya kawo misali da sako daya daga cikinsu mai suna Bashir Adam, mazaunin Tsallaken Dogo a Wusasa, bayan kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.
“Sai ga shi ko wata ba a yi ba Bashir ya fito daga gidan yari yana ci gaba da harkokinsa.
“Hakan ya canja tunanin mutane kwarai har wadansu daga cikin mazauna yankin sun fara kaura,” inji shi.
Bashir Adam ya ce Kotun Majistare da ke Birnin Zariya ce ta yanke masa hukuncin daurin shekara 14 ba tare da zabin biyan tara ba a ranar Talata 25 ga Janairun 2021, a karkashin Sashi na 247 (3) na Final Kod na dokar Jihar Kaduna.
Wani manomi da ke zaune a yankin Dutsen Abba, wanda aka fi kai hare-haren ta’addanci da ya bukaci a boye sunansa, ya ce ba da jimawa ba aka kai hari, har aka sace iyalan tsohon kansilan yankin kuma daga baya aka yi nasarar kama wadansu daga cikin wadanda suka kai harin.
Sai dai ya ce, “Bayan dan lokaci kadan da gama yawo da bidiyon wadanda aka kama, inda da bakinsu suka ce su ne suka aikata laifin, kwatsam sai aka gan su sun fito suna yawonsu a gari.
“Wannan ya tsorata mu fiye da hare- haren da suke kawo mana. Saboda na taka rawa sosai wajen kama su. Ka ga yanzu rayuwata tana cikin hadari ke nan.
“Da muka bincika, mun samu tabbacin cewa ’yan sanda sun kammala bincikensu sun kai wadanda ake zargin ga kotu. Daga nan ba mu san yadda aka yi ba, sai muka ji an sake su,” inji manomin.
Mutanen yakin sun ce tun ranar 31 ga Mayun bana, yankin ya yi ban-kwana da zaman lafiya, kuma wadanda aka fanso su daga hannun masu garkuwar sun ce wadanda kotunan suka saki ne shugabannin ’yan ta’addar a can daji, kuma dukkansu ’yan asalin yankin ne don haka sun san kowa.
Wadanda aka sako su ne Mu’azu Sani da Mubarak Adamu da Faisal Shehu da Yunusa Audi da Sani Igwa da kuma Abubakar Muhammad.
Haka al’ummar Unguwar Magume da ke Tukur Tukur a Karamar Hukumar Zariya, sun shaida wa Aminiya cewa matashin da aka kama kan zargin hada baki da ’yan bindiga su sace yayarsa mai suna Abubakar Haliru, wanda yayar ta ranta masa Naira miliyan 1 da dubu 400, shi ma an sako shi.
Shi ma an yi ta yada bidiyonsa a Intanet, lokacin da ’yan sanda suka baje kolinsu, inda ya tabbatar da aikata laifin tare da yin nadama, amma sai ga shi an ce an gan shi yana yawo a gari wanda hakan ya so haifar da tarzoma a Unguwar Tudun Jukun.
Al’ummar yankin sun ce tunda aka kama shi ba su daina bibiyar shari’ar ba sai da suka tabbatar ’yan sanda sun kammala bincike sun kai shi kotu, an tsare shi.
Sai dai sun ce ashe an kashe maciji ne ba a sare kansa ba, domin ba a dade ba sai suka samu labarin an sake shi, har ya dawo gida ya ci gaba da hidimominsa.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin wasu daga cikin kotunan amma ba wanda ya yarda ya yi bayani, sai dai wani ma’aikaci kotu da ya nemi a boye sunansa ya ce, su kansu suna zargin wadansu daga cikin alkalansu, kan irin wannan dabi’a.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya ce rundunar ba ta da hannu a kan sakin wadanda ake kamawa kan garkuwa da mutane.
Ya ce duk lokacin da ’yan sanda suka kama wanda ake zargi sukan gudanar da bincike su kai shi kotu.
Game da Abubakar Haliru da ake zargin an sako shi, Jalige ya jami’an musamman da ke yaki da ayyukan ta’addanci (IRT) suka kama shi suka gabatar da shaidar cewa sun kai shi kotu.
Ya ce rundunarsu ba ta da hannu a sakinsa domin sun kai shi kotu, kotu ta kai shi gidan yari kafin a ci gaba da shari’a, kuma daga bisani ta sake shi bisa dalilan da ta sani.
Wannan lamari ya tayar da hankalin Unguwar Magume da kewaye kamar yadda Yusuf Ibrahim na Sabuwar Unguwar Magume ya yi bayani, inda ya ce sakin ya yi matukar ba su mamaki saboda a cewarsa sakinsa da kotu ta yi akwai lauje cikin nadi ganin girman laifin kuma ga ikirarin da ya yi da bakinsa kowa ya ji, kuma an baje kolinsa tare da masu laifi irin nasa a Abuja a kwanakin baya.
Duk inda aka zaga akan tatar da mutanen yankin suna tattaunawa kan yadda hakan ke faruwa musamman sakin Abubakar Halliru.