Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana cewa kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta ba a yankin Arewa bane kawai ya shafi duk yankunan kasar.
Sarkin Musumin, ya kara da cewa zaman lafiyan Najeriya ne bukatarsu a kullum a matsayinsu na Sarakuna.
Ya kuma bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen taron Sarakunan Arewa da aka gabatar a ranar Litinin din nan a jihar Kaduna.
An kuma yi taron ne a gidan tarihi na Arewa da ke a jihar wanda kuma ya samu halartar Sarakuna daga yankin Arewacin kasar nan.
