✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba abin da tsarin karba-karba ya kawo wa Najeriya sai ci baya – Sule Lamido

Tsohon Gwamnan ya ce shi sam ba ya goyon bayan tsarin na karba-karba.

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Sule Lamido, ya ce sam ba ya goyon bayan tsarin karba-karba.

A yayin wata tattaunawarsa da sashen Hausa na BBC, tsohon Gwamnan ya ce babu abin da tsarin ya kawo wa Najeriya face koma-baya, inda ya yi kira ga jam’iyyu da su mayar da hankulansu wajen ci gaban kasa, ba abin da za su samu ba.

Sule Lamido ya ce yayin da Najeriya ke neman ci gaba, bai kamata a ci gaba da siyasar bangaranci ko kabilanci ba.

Ya ce, “Idan aka zo maganar karba-karba, ni babu ruwana da ita. A wannan lokacin, kamata ya yi mu fi mayar da hanlaki wajen yin siyasar ci gaba, kamar yadda ake a sauran kasashen duniya.

“Najeriya a matsayin kasa kamata ya yi ta mayar da hankali wajen hadin kan ’yan kasarta, zaman lafiya, ci gaba da kuma habaka tattalin arzikin mutanenta.

“Ni dai irin shugaban da nake so na gani ke nan. Duk wanda ke kokarin Najeriya ta zama babbar kasa, shi ya kamata a tallafawa, ba tare da la’akari da inda ya fito ba, addini ko kabilarsa. Irin mutumin ke nan da ya kamata dukkanmu mu goyi baya. Ka duba kasar mu a yau ka gani, ina tsarin karba-karba ya kai mu?” inji tsohon Gwamnan.