✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ba a taba shugaba mai farin jini kamar Buhari ba a Najeriya —Adesina

Adesina ya ce a Buhari ya fi Malam Aminu Kano yawan masoya.

Hadimin Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Femi Adesina, ya ce babu wani dan siyasa a tsawon tarihin Najeriya da ya fi Shugaba Muhammadu Buhari farin jini a wurin jama’a.

Adesina ya ce yadda mutane ke dandazon ganin Buhari ya zarce na fitattun ’yan siyasa da suka yi fafutikar samun ’yancin Najeriya irin su Malam Aminu Kano da Nnamdi Azikiwe, Obafemi Awolowo da sauransu, wadanda har yanzu, shekaru da dama bayan rasuwarsu, ana ci gaba da ganin su da daraja.

“Na ga ’yan siyasa irin su Aminu Kano, Shehu Shagari, MKO Abiola, Bashir Tofa, Awolowo, Azikiwe, da sauransu.

“Amma ban taba ganin mai firin jini kamar Buhari ba, wanda mutane ke rububin ganin shi a kowane yanki na Najeriya,” inji Femi Adesina.

Ya ci gaba da cewa, “Na zaga kasar nan tare da shi (Buhari), mun kuma je kasashe da dama tare; Ni dai ban ga wani shugaba a Najeriya a da ko a yanzu ba da ya kai Buhari jan hanklin mutane.”

Ya bayyana hakan ne a wata makala da ya rubuta inda ya bayyana goyon bayansa ga kalaman Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, cewa Buhari ne dan siyasa mafi farin jini a Najeriya.

Osinbajo ya yi furucin ne a yayin da yake ganawa da jakadu a Ofishin Jakadnacin Najeriya da ke birnin Landan na kasar Birtaniya makon jiya.

A cikin rubutun, Adesina ya ce, “Osinbajo mutum ne amintacce, saboda haka ku dauki duk abin da ya fada da muhimmanci.

“Za a iya cewa ai dole mataimakin shugaban kasa ya ce haka game da uban gidansa, ya rika koda shi a bainar jama’a saboda uban gidan ya goyi bayansa idan zai nemi takarar shugaban kasa.

“Abin da duk dan siyasa mai hankoron neman wani abu zai yi ke nan, amma duk wanda ya yi aiki da Buhari da Osinbajo ya san ba haka yake ba.

“Shi mutum ne kaifi daya, mai tsage gaskiya kuma mai tawakkali ga Allah; Babu abin da ya dauka a matsayin na a mutu ko a yi rai; Idan ya ga dama zai iya yin shiru game da abin da ya fada a kan Buhari saboda kar a yi masa mummunar fahimta.

“Maganar da ya yi cewa da alama Buhari Buhari ne dan siyasa mafi farin jini tsawon lokaci, na yarda, ba wai don shi ya fada ba, a’a saboda ni ma ganau ne.

Ya ce “A tsawon shekaruna na ga ’yan siyasa irin su Aminu Kano, Shehu Shagari, MKO Abiola, Bashir Tofa, Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe, da sauransu.

“Amma dai ban taba ganin mai firin jini kamar Buhari ba, wanda mutane suke cincirindo kamar kudan zuma domin su ganin shi a kowane yanki na Najeriya.

“Na zaga kasar nan tare da shi. Mun kuma je kasashe da dama tare ni dai ban ga wani shugaba a Najeriya a baya ko a yanzu, da ya kai Buhari, jan hanklin mutane.

“Saboda Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo bai yi kuskure ba da ya siffanta shi cewa shi ne ‘dan siyasa mafi farin jinni da aka samu a tsaon shekaru’.”

Adesina ya kafa hujja da yadda ’yan Najeriya da dama su yi ta tururuwar fitowa kan tinuna suna murna a lokacin da Buharin ya dawo daga duba lafiyarsa da ya dauki tsawon lokaci a kasar Birtaniya a shekarar 2017.