✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Baƙuwar cuta ta kashe ƙananan yara 5 a Nasarawa

Kananan yara biyar sun rasu cikin kasa da awa 24 sakamakon wata bakuwar cuta a Karamar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa

Aƙalla ƙananan yara biyar ne aka tabbatar sun rasu cikin kasa da awa 24 sakamakon wata baƙuwar cuta a Ƙaramar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa.

Babbar Jami’ar Binciken Cututtuka ta Jihar Nasarawa, Dokta Grace Tsakpa, ta tabbatar da mutuwar kananan yaran, inda ta ce an tura jami’an lafiya zuwa yankin domin gudanar da bincike.

Ƙauyen Gidinye da ke yankin Jenkwe na daga cikin wuraren da aka samu ɓullar wannan baƙuwar cutar mai kisa.

Wakilin Aminiya ya gano cewa yaran shekarunsu 5 ne zuwa 15, kuma sun yi fama da ciwo ciki da ciwon kai da amai da gudawa a ranakun Litinin da Talata kafin su rasu.

Sakataren Yaɗa Labaran Ƙungiyar Matasan Magili, Mista Samuel Akala,  ya shaida wa wakilinmu cewa, yaran da suka rasu, sun bar gida tare da iyayensu zuwa gona a kusa da Karamar Hukumar Keana ne, inda a can suka fara rashin lafiya.

A cewarsa, “Cikin ƙasa da awa 24 muka rasa ƙananan yara biyar a yankin nan.

“Sun je gona da iyayensu, a can ne ɗayasu ya fara kukan ciwon kai, ya fara amai da gudawa a ranar.

“Kafin a daɗe numfanshinsa ya fara sarƙewa, shi ne aka kawo shi gida, a nan ya rasu.

“Sauran yaran ma irin wannan alamar suka nuna kafin su rasu, kuma abin ƙaruwa yake yi, duk da cewa ba mu san ainihin dalilin mace-macen ba.

“Muna roƙon Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHCDA) da Hukumar Yaƙi da Yaɗuwar Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) su gudanar da bincike a ƙananan hukumomin Obi da Keana, domin ganowa da shawo kan wannan baƙuwar cuta,” in ji shi.

Daga nan ya buƙaci gwamnati da sauran hukumomin Jihar Nasarawa su ɗauki matakan gaggawa domin ceto rayuka da kuma hana yaɗuwar cutar.
Babbar jami’ar binciken cututtuka ta jihar, Dr. Grace Tsakpa, ta ce, duk da cewa sakamakon gwaje-gwajen da aka gudanar bai fito ba, amma ana zargin  cutar na da alaƙa da gubar abinci, saboda alamomin cutar sun fara bayyana ne bayan yaran sun gama cin abinci a gona.