✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi: Gwamnatin Kano ta bai wa dalibai hutun sati 3

Gwamnatin ta bai wa daliban hutun ne saboda watan Ramadan.

Gwamnatin Jihar Kano ta bai wa dalibai hutun sati uku albakarcin azumin watan Ramadan.

Sanarwar hakan da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Aliyu Yusuf ya fitar ranar Alhamis ta umarci iyaye da ke da yara a makarantun kwana da su je domin daukar su da safiyar ranar Juma’a.

A cewarsa, daliban makarantun kwana za su koma makarantunsu a ranar 30 ga Afrilu, a yayin da daliban ’yan je-ka-ka-dawo za su koma ranar 2 ga watan Mayu.

Ya yi gargadin cewa za su dauki matakin ladabtarwa a kan duk wadanda suka saba umarnin.

“Dalibai da iyaye su tabbatar da bin ka’idojin da aka gindaya na komawa makaranta,” in ji sanarwar.