✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi (8)

Dalilan yin azumi: Muna daukar lokaci mu yi koyarwa a kan batun yin azumi domin masu bi day awa sun manta da muhimmancin yin azumi…

Dalilan yin azumi:

Muna daukar lokaci mu yi koyarwa a kan batun yin azumi domin masu bi day awa sun manta da muhimmancin yin azumi da addu’a, akwai wadansu da suke ganin kamar yin azumi ba lallai ba ne a gare su, saboda haka sun manta ranar da suka yi azumi domin su nemi fuskar Ubangiji Allah game da wani abu ko game da rayuwar wadansu.
Makon jiya, mun yi karatu daga cikin Littafi Mai tsarki – Joel 2:12 – 17 ayoyin da ke cewa “Amma ku yanzu, inji Ubangiji, ku juyo mini da dukan zuciyarku, tare da azumi da kuka da bakin ciki: ku tsaga zukatanku ba tufafinku ba, ku juyo wurin Ubangiji Allahnku: gama Shi Mai alheri ne, cike yake da juyayi, Mai jinkirin fushi, Mai yalwar, Yana sake nufinSa a kan masifar da Ya shirya. Wa ya sani ko ba za ya sake nufinsa ba, ya bar albarka a bayansa, wato hadaya tagari da ta shaga Ubangiji Allahnku? A busa kaho cikin Sihiyona, a tsarkake kwanakin azumi, a tattara taro mai saduda, a tara mutane, a tsarkake jama’a, a tattara dattawa, a tattara yara da wadanda ke shan nono, bari ango ya fita dakinsa, amarya kuma daga cikin lolokinta. Bari Priest, masu hidimar Ubangiji, su yi kuka tsakanin haraba da bagadi, su ce, kada ka bada gadonka zuwa zargi, har da al’ummai za su mallake su: don mene ne za su ce a cikin dangogin mutane za su ce ina Allahnsu?”
Mutane da yawa suna cikin bauta domin zunubi, sun kuma gagara fita daga ciki, suna cikin wahala sosai domin Shaidan mugu ne kuma ba ya da tausayi ko na kwabo a cikinsa. A inda muka yi karatu, za mu ga cewa, ’ya’yan Isra’ila sun zama abin tausayi, kariyar da Ubangiji Allah ke ba su, Ya janye; magabta suka auko musu; suka kuma ci nasara bisansu. Sai mu lura zunubi yakan kai mutum zuwa ga bauta karkashin ikon Shaidan, wannan ba abin wasa bane: watakila mai karatu ya lura da cewa akwai wani zunubi da yake aikatawa, sau da dama kakan yi kudiri cikin zuciyarka cewa ba za ka sake aikata wannan zunubi ba, amma sai ka lura cewa, wannan kyakkyawar niyya na dan lokaci kadan ne kawai, ba ta dadewa.
Kullum kana cikin addu’ar tuba amma har yanzu kana fama da wannan zunubi, sai ka ga kamar wannan ya fi karfinka, bari in ba ka shawara da za ta taimake ka sosai, ka dauki kwanakin azumi tsakaninka da Allah, bisa ga yadda ka ji a cikin ruhunka, tare da addu’a, Allah cikin alherinSa, zai kawo karshen irin wannan hali cikin rayuwarka. Irin wannan halin zunubi zai bar ka ne kawai idan ka natsu cikin azumi da addu’a da kuma binciken Littafi Mai tsarki; musamman wuraren da Allah Ya yi magana a kan irin wancan zunubi. Azuma kan sa mu kawo tunaninmu da hankulanmu a kan abin da muke addu’a a kai, haka nan Allah cikin ikonSa zai barrantar da kai daga cikin kuncin da Iblis ya sa ka ciki.
Za ka iya yin azumi domin wani da ka sani yana fama da irn wannan wahala, idan ka lura ko kika lura cewa wani da ka sani ko kika sani, yana fama da irin wannan wahala na ci gaba da aikata abubuwa marasa kyau, za ka iya daukar kwanakin azumi da addu’a domin sa ko dominta. Misali idan kina da aure, sai kika lura cewa maigidanki yana shan giya, ko yana neman mata a waje, hanyar taimakon irin wannan mutum, ba lallai fada ba ne, idan ka yi wa irin wannan mutane fada za ka sake tura su ne cikin miyagun ayyukan da suke yi, amma idan kin dauki lokaci domin yin azumi da addu’a a madadinsa, aikin gyara shi, ya fita daga cikin hannunki, kin kuma damka shi a hannun Ubangiji Allah; babu wani abin da ya fi karfin Allah. Allah da kanSa zai juyo da tunaninsa, ya ga cewa ba ya kuma sha’awar irin wannan rayuwa. Haka nan za mu iya yin azumi da addu’a domin iyalai da kuma kasassu daban-daban; musamman wuraren da suke cikin mawuyacin hali, kamar kasasshe da suke cikin yaki. kasarmu Najeriya da muke fada da rashin kwanciyar hankali na shekaru. Gaskiya masu bi, mun manta da babban makamin da muke da shi, wannan makamin kuwa shi ne azumi da Addu’a. Mu tashi, mu yi amfani da shi, idan muka yi amfani da addu’a tare da azumi, za mu ci nasara bisa kowane aikin mugunta.
Neman nufin Allah game da kiransa a kan rayuwarmu:
Kowane mai bin Yesu Kiristi, yana da aikin da Ubangiji Allah Ya shirya da zai yi a cikin wannan duniya, kuma za mu iya sanin wannan aiki idan mun kawo kanmu gaban Ubangiji Allah cikin azumi da addu’a. A cikin Littafin Matta 3:16 da 4 :1- 2, maganar Allah na cewa “Yesu kuwa, sa’anda aka yi masa baptisma, ya fita nan da nan daga cikin ruwa: ga kuwa sammai suka bude masa, Ya ga Ruhun Allah yana sabkowa kamar kurucya yana zuwa bisansa”….. “Sa’annan, Ruhu ya tafi da Yesu cikin jeji domin Shaidan shi yi masa jarrabawa. Sa’anda ya yi azumi yini arba’in da kwana arba’in, daga baya ya ji yunwa…” Luka 4:15 – 21, “Ya yi koyarwa cikin majami’unsu, yana da daraja wurin dukkan mutane, ta zo Nazarat inda aka goye shi, ya shiga cikin majami’a bisa ga al’adatasa ran asabaci, ya tashi tsaye garin ya yi karatu. Aka mika masa Littafin Annabi Ishaya, ya bude littafi, ya iske wurin da aka rubuta, Ruhun Ubangiji yana bisa gare ni, Gama an shafe ni da zan yi shelar bishara ga talakawa: Ya aike ni domin in yi ma damrarru shela ta saki, Da mayaswar gani ga makafi, In kwance wadanda an kuje su In yi shelar shekara ayyananniya ta Ubangiji. Ya nade littafi, ya mayar ma mai hidimar, ya zauna; dukansu cikin majami’a suka zuba masa idanu. Ya fara ce musu, Yau an cika wannan nassi a cikin kunnuwanku.” Ayyukan Manzanni 9:6; “Amma ka tashi ka shiga cikin birni, za a fada maka abin da za ka yi. Kwana uku ba ya gani, ba ya kuwa ci ko sha. Amma akwai wani mai bi cikin Dimashka, ana ce da shi Hananiya; Ubangiji ya ce masa cikin Ruya, Hananiya, shi kuwa ya ce, Ga ni Ubangiji. Ubangiji ya ce masa, Tashi ka tafi cikin Hanya wadda ana ce da ita Mikakkiya a cikin gidan Yahuda, sai ka yi tambayar mini mutum, sunansa Shawulu, mutumin Tarsus: gama, ga shi, yana addu’a”.
Idan muna so mu san ko mene ne Allah Yake so mu yi a cikin wannan rayuwar ta duniya, za mu gane cikakke idan har mun nemi nufinSa cikin Azumi da addu’a. Da dama muna kiran kanmu masu bi amma gaskiyar ita ce, ba mu ma san ko mene ne nufin Allah game da rayuwarmu ba, kuma ba mu kula mu sani ba. Mu dauki lokaci da kuma kwanaki na azumi da addu’a domin mu san abin da Allah Yake so mu yi a cikin wannan duniya. Idan Allah Ya yarda, mako mai zuwa; za mu yi nazari a kan albarkan da ke cikin yin azumi.
Jama’a, kada mu manta kawo wannan kasa tamu gaban Ubangiji Allah cikin addu’a da azumi. Allah Ya ba mu zaman lafiya, amin.