Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) a ranar Alhamis ta bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta addabi sassan ƙasar nan kwanan nan ta shafi jihohi 34 da ƙananan hukumomi 217, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 321.
NEC ta kuma ce mutane 1,374,557 abin ya shafa, yayin da mutane 740,743 suka rasa matsugunansu a faɗin ƙasar.
- Yara masu zanga-zangar yunwa sun sume a kotu
- ’Yan fashin daji sun sace matafiya 20 a hanyar Kontagora
Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja bayan kammala taron NEC ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima.
Ya ce, ambaliyar ta kuma yi sanadin raunata mutane 2,854 tare da lalata gidaje 281,000 da kadada 258,000 na gonaki.
Ya kuma ce NEC ta umurci ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar mahalli da ta fara gudanar da bincike ga magudanan ruwa da madatsun ruwa na Nijeriya a wani mataki na daƙile illar ambaliyar ruwa.
Ya ce, Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Mahalli, Farfesa Joseph Utsev, ya yi wa majalisar NEC bayanin ayyukan shiga tsakani da gwamnatin tarayya ke yi a faɗin ƙasar nan dangane da illar ambaliyar ruwa ta bana wadda ta zama babban ibtila’i a ƙasar.