✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya ƙi janye ƙudirin ƙara haraji

Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki kan ƙudirin ƙara haraji.

Shugaba Bola Tinubu ya yi watsi da shawarar Majalisar Tattalin Arziki (NEC) wadda ta nemi ya janye ƙudirinsa na ƙara haraji.

Kazalika, ita ma Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta bayyana adawarta da ƙudirin tana mai cewa ya saɓa wa muradun jama’ar Arewacin ƙasar.

Yayin zaman da ta gudanar a ranar Alhamis, NEC ta ba shawarar jingine ƙudirin ƙara haraji domin buɗe ƙofar tuntuɓar dukkanin masu ruwa da tsaki.

Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Juma’a, Tinubu ya buƙaci NEC da ta bari a aiwatar da sabuwar dokar ta ƙara haraji.

Sanarwar wadda ta yaba wa Majalisar Tattalin Arzikin dangane da shawarar da ta bayar, ta kuma tunatar da ita muhimmancin ƙara harajin domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Dangane da hakan ne Tinubu yake tunatar da duk masu bore a kan ƙudirin da ya riga da aike wa Majalisar Tarayya da cewa har yanzu ƙofar tuntuɓe-tuntuɓe ga masu ruwa a buɗe take.