✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tinubu ya naɗa muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa

Manjo Janar Olufemi Olatubosun Oluyede zai ci gaba da riƙe muƙamin zuwa dawowar Lagbaja.

Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Manjo-Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin muƙaddashin Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Olufemi zai ci gaba da riƙe muƙamin har lokacin da Manjo-Janar Taoreed Lagbaja zai dawo ƙasar.

Kafin naɗa shi a muƙamin, Oluyede ne Kwamanda Makarantar Horas da Mayaƙan Ƙasa ta rundunar da ke Jaji a Jihar Kaduna.

Mai shekaru 56, Manjo Janar Oluyede abokin karatun Lagbaja ne a Makarantar Horas da Ƙananan Hafsoshin Soji (NDA) inda aka yaye su a shekarar 1992.

Ya rike muƙamai da dama da suka hada kwamandan da mataimakin kwamandan a matakainda rundunoni da dama kafin yanzu.

Tun a makon da ya gabata rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya ta bayyana cewa Janar Lagbaja yana jinya a wani asibiti a ƙasar waje bayan da farko ta musanta rahotonnin da ke cewa ya rasu.

A lokacin ta bayyana cewa daraktan tsare-tsare na rundunar, Manjo Janar Abdulsalami Ibrahim ne yake jagorantar harkokinta matsayin riƙo.

Daga baya Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta musanta batun, inda ta ce “babu wani batun muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa” a tsarin aikinta.