✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi (2)

Yaya ake yin azumi?: Azumi ba janyewa daga cin abinci kadai ba ne amma mu iya kafa tunaninmu a kan Ubangiji Allah, tsarkinSa, mulkinSa da…

Yaya ake yin azumi?:

Azumi ba janyewa daga cin abinci kadai ba ne amma mu iya kafa tunaninmu a kan Ubangiji Allah, tsarkinSa, mulkinSa da kuma nufinSa. A koyaushe idan mutum ya koshi da abinci; to, sha’awar jiki na karuwa sosai, haka duk fannin rayuwar mutum, cikin tunaninsa, cikin nufinsa, har ga yadda yake son yin abubuwa. Amma lokacin yin azumi duk sha’awar jiki da kwadayin rayuwa sukan ragu kwarai da gaske; sai ruhun mutum ya samu dalilin zumunci da Ruhun Ubangiji Allah. Ga kowane mai bin Yesu Kiristi wanda yake da natsuwa kuma ya sa kai sosai cikin wannan ibada ta yin azumi, zai ga cewa yana iya gane abubuwa na ruhaniya da sauki a irin wannan lokaci fiye da lokacin da ba ya yin azumi. Shi ya sa mai bin Yesu Kiristi wanda ba ya yin azumi ba zai iya sakankance abubuwa na ruhaniya a sauwake ba. Idan mai bin Yesu Kiristi ya yi azumi na fiye da kwan ashirin zuwa sama; zai ga cewa duk duniya da sha’awar da ke cikinta, wofi ne kawai, a irin wannan lokaci za ka gane rashin muhimmancinsu a cikin rayuwarka ta yau da kullum. A lokacin azumi, mutum yakan kusanci Allah cikin tunani, cikin yadda yake yin abubuwa, mutum sai ya kallafa ransa cikin yin abin da zai gamshi Ubangiji Allah, wannan ya kunshi yin biyayya ga maganar Allah, za mu zama da sha’awar jin abin da Allah ke cewa a kullum. Mutum zai ga cewa idan ka dauki Littafi Mai tsarki ka soma karantawa, za ka samu sabon hasken ganewa a ciki, idanunka za su budu, za ka ga sabon abu wanda ba ka taba yin tunani a kansa ba samsam. Azumi na kara iko irin na ruhaniya kwarai; ina so mu sani cewa addinai da yawa suna yin azumi, kuma duk lokacin da suka yi azumi irin nasu, su ma suna samun karuwa sosai da irin ikon ruhun da suke bautawa, shi kuwa zai karfafa su sosai har su iya yin abin da zai gamshi shi wanda suke bautawa. Amma ga kowane mai bada gaskiya ga sunan Yesu Kiristi, idan har ya samu wannan ceto babu shakka Ubangiji Allah zai ba shi iko bisa ikon Iblis ko Shaidan da kansa. Yawancin masu bin Yesu Kiristi ba su da lokacin yin azumi a cikin shirin rayuwarsu ko ma na dan lokaci kadan, irin wadannan mutane ba karamar asara ne suke yi ba. Azumi kamar kai kuka ne ga Ubangiji Allah, musamman ma lokacin da muka fuskanci kalubale cikin rayuwar yau da kullum. Duk lokacin da ka ji kamar Ruhun Allah na bishe ka, ka dauki azumi ko na kwana daya ne, kada ka yi jinkiri; ka yi biyayya kawai kuma babu shakka za ka ga albarka wadda za ta biyo baya.
Azumi abu ne wanda Yesu Kiristi yana son dukan masu binsa su rika yi a koyaushe; babu wani kayadajjen lokacin da ya kamata a yi azumi, koda yake mutane da yawa sun dauki gurbin Yesu Almasihu cewa da yake ya yi azumi na kwana arba’in ya kamata masu binsa su ma su yi azumi na kwana arba’in; ba lallai haka ba; amma bisa ga yadda Ruhun Allah ya bi da mutum, haka nan mutum zai aikata. Idan bisa ga bishewar Ruhu mai tsarki, ka gane cewa ka yi azumi na kwana arba’in, to ba laifi ba ne, amma ba wai umurni ne daga wurin Ubangiji Allah ba, wani lokaci ma na kwana uku ne Ubangiji zai bi da mutum, wani lokaci na kwana daya ne kawai.  Duk ya danganta ne ga yadda muke tafiya da Allahnmu. A cikin Littafin Matta 6:16–18, maganar Allah na koya mana cewa “Kuma lokacin da kuke yin azumi, kada ku kwansare fuskarku, kamar yadda masu riya ke yi, gama suna bata fuskokinsu, domin mutane su ga suna azumi. Gaskiya nake ce muku, sun rigaya sun karbi ladarsu. Amma kai, lokacin da kake yin azumi, shafe kanka da mai, ka wanke fuskarka. Domin kada ka bayana ga mutane kana azumi, sai Ubanka da ke gani daga cikin boye kuwa , za ya saka maka.” Yesu Kiristi ya yi koyarwa game da yadda mai binsa zai yi azumi, daga inda muka yi karatu, za mu iya tsintar tambayoyi muhimmai guda biyu akalla: Tambaya ta farko ita ce: Yaya mutum ya kamata ya kasance lokacin yin Azumi? Tambaya ta biyu kuma ita ce: Shin wane ne ya kamata ya ga azumin da muke yi? A tambaya ta farko, za mu lura cewa a cikin koyarwar Yesu Krista, ya kasa su kashi biyu: da farko ya ce, akwai azumi na masu riya, akwai kuma azumi irin na ’ya’yansa; masu binsa. Yin azumi ba lallai ne yana nuna cewa kai mai tsoron Allah ba ne, abin la’akari shi ne duk addinai suna yin azumi kuma suna da dalilansu daban-daban na yin azumin. Yayin da Yesu Kiristi yana koyarwan nan, yana duba yadda farisawa suke yin nasu azumin, idan suna azumi; suna kwansare fuskansu domin su nuna wa dukan jama’a da suke kewaye da su cewa su masu ibada ne; suna kokari su ga cewa sun bambanta da duk wadanda suke kusa da su, amma Yesu Kiristi ya ce dukan wanda zai yi irin wannan azumin, ya sani cewa tsakaninsa ne da Allah kawai. Duk mai bin Yesu Kiristi wanda ya son yin azumin da za ta gamshi Ubangiji Allah, dole ya lura da yadda zai bayyana a gaban mutane, ya kamata ya zama da tsabta a jiki da kayan da yake sanye da shi, ya yi wanka, ya shafa mai a fuskarsa domin kada bakinsa ya bushe, ya goge hakorinsa da bakinsa domin kada bakinsa ya yi wari. Abu na biye shi ne; wane ne ya kamata ya ga cewa muna yin azumi? A nan ma Yesu Kiristi ya raba shi kashi biyu: na farko su ne wadanda suke yin azumi domin mutane su gani cewa suna yi azumi, suna yin kokari sosai domin wadansu mutane su kula da su. Damuwarsu shi ne akwai wadanda suka gan ni kuwa lokacin da nake yin wannan azumin ko kuwa babu? Ba sa jin dadi ba ko kadan idan ba wani wanda ya gan su ya kuma ce musu sannu da kokari ba. Duk na Yesu Kiristi ne; tunaninsu daya ne kawai yadda za su ga fuskar Allah su kuma bidi nufinSa ba tare da sanar da kowa ba. Idan kuwa muka yi haka, Allah Ubangijinmu zai saka mana da alherinsSa. Idan Allah Ya bar mu a cikin masu rai mako mai zuwa za mu ci gaba da wannan koyarwa. Kada mu manta da ci gaba da yin addu’a domin kasarmu. Ubangiji Allah Ya taimake mu duka, amin.