Ya tabbata Rishi Sunak shi ne sabon Fira Ministan Birtaniya bayan Liz Truss wadda ta yi murabus kwannan nan.
Ga wasu muhimman ayyukan da sukan rataya kan duk wanda ke rike da mukamin Fira Minista na Birtaniya:
- Magidanci ya fara tattaki daga Gombe zuwa Abuja saboda Tinubu/Shettima
- ’Yan sumoga sun kashe jami’in Kwastam a Kwara
Ayyukan Fira Minista
Fira Minista ke jagorantar harkokin gwamnati kuma shi ne shugaban jam’iyyar da ta lashe babban zabe.
Yana da cikakken iko wajen gudanar da dukkan ayyukan gwamnati da daukar matakan da suka shafe ta.
Shi ke da hakkinsa nada ministocin da za su taimaka masa wajen gudanar da gwamnati. Yana da ikon nadawa da sauke minista a kowane lokaci.
Tare da hadin gwiwar Shugaban Kasa, Fira Minista ke da hakkin tarawa da yadda za a kashe kudaden shiga.
Fira Minista tare da ministocinsa na iya samar da sabuwar doka muddin suka samu amincewar majalisar dokoki.
Ikon Fira Minista
Duk ma’aikatun gwamnati da ma’aikatansu na karkashin ikonsa ne.
Yana da karfin ikon daukar mataki kan abin da ya shafi fannin tsaron kasa.
Sai da umarninsa kasa za ta yi amfani da makaman kare-dangi, da kuma harbowa ko kama duk wani jirgin saman da aka yi fashi ko ba a san da zamansa ba a sararain samaniyar Birtaniya.
Yana da ikon mika lambar karramawa ta kasa ga wanda ko wadanda suka cancanta.
Yakan gana da Sarkin Inglila a duk mako domin sanar da shi yadda harkokin gwamnati ke tafiya. Wannan ganawar ta sirri ce tsakanin su biyun.
Albashin Fira Mimistan Birtaniya
A matsayin Fira Ministan Birtaniya, albashinsa na kaiwa Fam 164,080 — Fam 84,144 a matsayin dan Majalisa da kuma karin Fam 79,936 a matsayinsa na mai rike da ofishin Fira Minista.
Wurin zama
Yana zama da kuma gudanar da aikinsa ne a inda aka gina domin zaman duk mai rike da mukamin. Wato gida mai lamba 10 da ke Downing Stree. Wuri ne da aka fara ginawa tun shekarar 1735.
Sai dai, wadanda suka rike mukamin a baya-bayan nan, ciki har da Boris Johnson sun zabi zama a gida mai lamba 11 da ke yankin saboda yalwarsa.
Fira Minista na da gidan gwamnati da ake ira Chequers a Buckinghamshire.
Albashin tsofaffin Firan Minista
A shekara, kowane tsoho Fira Ministan na karbar abin da bai gaza Fam 115,000 ba.
Akan biya su ne saboda gudummawar da suke bayarwa wajen gudanar da harkokin gwamnati.
Sai dai ba kowannensu ake biya ba face wadanda gwamnati mai ci ke yi da su.
Yadda Fira Minista ke fuskantar tuhuma
Duk da karfin mulkin da yake da shi, Fira Minista ba shi da damar yin gaban kansa a duk abin da ya ga dama, dole yana bukatar amincewar akasarin takwarorinsa saboda sai dai amincewarsa dokoki suke tabbata.
Idan kudurori da tsare-tsaren da fira minista ya gabatar suka fiye rasa goyon baya, majalisa na iya gabatar da kudurin yanke kauna daga gwamnatinsa — Idan hakan ta tabbata, to yana fuskatar barazarn sake gudanar da babban zabe.
Abin da ya faru da Misis Truss ke nan a kwanan nan, inda ta yi murabus saboda kudurorin da ta gabatar na inganta tattalin arzikin kasar sun gaza samun karbuwa ga yawancin ’yan majalisar.