✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ayyana takarar Osinbajo ko a jikina —Tinubu

Babu abin da ya dame mu da mayar da hankali akan wasu da ke sha’awar tsayawa takarar.

Jagoran jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ko gezau ba ya yi dangane da ayyana takarar Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo na neman kujerar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar su.

Sanarwar da shugaban kungiyar SWAGA da ke fafutukar ganin Tinubu ya tsaya takarar shugabancin kasar, Sanata Dayo Adeyeye ya gabatar ta ce abinda suka mayar da hankali akai a wannan lokaci shi ne tallata dan takarar na su, amma ba mayar da hankali akan wasu da ke sha’awar tsayawa takarar ba.

Kungiyar SWAGA da ke kokarin tabbatar da manufofin siyasar Jihohin da ke Kudu maso Yammacin Najeriya ta ce alkalami ya riga ya bushe dangane da takarar Tinubu wanda ya game kowanne sashe na kasar.

Shi kuwa shugaban kungiyar goya wa Tinubu baya ta TSG kuma dan Majalisar Wakilai, James Faleke ya bayyana cewar ganin yadda dan takarar na su ya karbu tsakanin ’yan siyasa da Sarakunan da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, babu wani dan takarar da zai iya kalubalantarsa wajen karawa da shi domin samun tikitin jam’iyyarsu ta APC.

Shi kuwa kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Lagos Seye Oladeji ya ce kansu a hade yake wajen ganin Tinubu ya cimma muradun san a zama shugaban Najeriya a shekara mai zuwa.