Gwamnatin Tarayya ta ce babu bukatar ayyana dokar ta-baci kan matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.
Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammadu Maigari Dingyadi, ne ya sanar da hakan bayan kiraye-kirayen ’yan Najeriya ga gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci domin magance matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma, inda ’yan bindiga ke kai hare-hare tare da garkuwa da mutane domin karbar kudaden fansa.
- Yadda sojoji suka ragargaji Turji da yaransa a Sakkwato
- An kama bindigogi 35 da masu muggan laifi 245 a Kano
Ya ce ko da yake tsarin dimokuradiyya ake bi a Najeriya kuma kowa na da ’yancin fadin ra’ayinsa, “Amma ba mu da aniyar ayyana dokar ta-baci a kan wannan lamari.”
A cewarsa, sanya dokar da rashin sanyawa babu abin da zai canza a yanayin tsaro a Najeriya.
“Ko an ayyana dokar ta-baci ko ba a ayyana ba, abin da kawai ake bukata shi ne samar da wadataccen tsaro.
“Abin da aka yi ke nan a wasu bangarori da aka ayyana dokar ta-baci, kamar bangaren ilimi, amma idan aka lura babu abin da ya sauya.
“Ko an sanya dokar a kan matsakar tsaro ko ba a sanya ba, babu wani sauyin da za a gani,” inji ministan.
Sai dai ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta dauki matakan da suka dace domin magance matsalar, ba sai lallai ta sanya dokar ta-baci ba.
Ya ce, “Idan ma a sanya dokar mutane za ta shafa ta hana su fita neman halaliyarsu ba tare da an samu biyan bukata ba. Mu dai za mu yi abin da ya dace, kuma da yardar Allah za mu yi nasara,” inji shi.
Ya bayyana haka ne a zantawar da Sashen Hausa na BBC ya yi da shi a game da karin albashin ’yan sanda da Gwamnatin Tarayya ta yi.