✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Aure ya kusa ya kullu tsakanin Ummi Rahab da Lilin Baba

Jarumar ce dai ta wallafa sakon hakan a shafinta na Instagram

Alamu na nuna cewa mawaki kuma jarumin da ya dauki nauyin fim din Wuff mai dogon zango ya kusa ya yi wuff da jarumar da ke jan fim din, Ummi Rahab.

A kwanakin baya Wata Sabuwa ta ruwaito akwai soyayya a tsakanin jaruman biyu.

A makon jiya ne jarumar ta kara rura wutar rade-radin da ake yi, inda ta wallafa a shafinta na Instagram bayan ta sa hoton Lilin Baba cewa, “Masoyina kuma mijina kuma Aljannata.”

Sai dai a kasan rutubun nata, an mayar
da maganganu, inda Ali Artwork ya ce, “Insha Allah.”

Shi ma Murtala Bloko ya ce, “Wanda ba zai iya gani ba ya kau da idonsa.”

Shi ma wani mai suna Real Adam M Ibrahim ya ce, “Dan bakin ciki sai ya mutu, amma fa ban kama suna ba.”

Wadannan maganganu da aka yi ana zargin da Adam M. Zango ake yi wa habaici, duk da cewa akwai Murtala Bloko a ciki, wanda shi kuma na hannun damar Adamun ne.

Idan ba a manta ba, an samu sabani mai zafi a tsakanin tsohon ubangidan Ummi Rahab, wato Adam A. Zango da ita, inda a lokacin Adamu ya ce ya rabu da ita ce saboda ba ta jin magana, ita kuma ta ce nemanta ya yi da soyayya, ita kuma ta ki amincewa.

Idan mutane suka lura, yanzu kusan wakokin Lilin Baba da fim dinsa kawai jarumar take fitowa.

%d bloggers like this: