Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon mun kawo muku mukalar da AbuMaryam AbdulRahman ya yi a kan iyayen da suke dora nauyi a kan ’ya’yansu mata da suke karatu a makarantun gaba da sakandare, ko kuma suke hidimar kasa. Muna fata za ku karanta don fa’idantuwa da darussan da ke cikinta.
Tun daga fitowar rana har zuwa faduwarta babu mai shakka akan cewa amfanin zunubi romonsa. Babu kuma wani mai shakka akan cewa Idan hagu ta kiya, to ya kamata a koma dama, Kuma kowa ya san cewa kiwon da ya karbi wani ba shi ne zai karbi wani ba. Babu wanda bai san amfanin aure shi ne zaman lafiya ba. Duk auren da aka ce babu zaman lafiya tsakanin mata da miji, to lallai ba shi da wani amfani, domin babu wani abu mai amfani da za a iya samu a cikinsa.
Idan aka ce auren dole a wannan zamani, a tawa fahimtar ana nufin, aurar da yarinya ga wanda ba shi ne ta zaba wa kanta ba. Sai mutane suke ganin wannan a matsayin cin zarafin yarinyar da kuma rashin wayewa ne. Amma a gaskiyar zance, ni na fi ganin cin zarafi ga yarinyar da ta nema wa kanta mijin aure ba tare da mahaifanta ne suka yi ruwa suka yi tsaki a wajen tantance shi ba, ko ma fito mata da wanda ya fi dacewa ta aura ba.
Babu laifi mace ta ga tana son wani ba, amma za ka gano an nade lauje cikin nadi idan ka tambayi yarinya me ya sa take son saurayin. Sai dai don kana da cikakken sani akan ka’idar da manzon Allah (SAW) ya bayar, wadda ya ce a bi ta wajen zaben miji, za ka sha dariya har sai cikinka ya yi ciwo. Za ka tabbatar da idan aka bar wannan baiwar Allah da tunanin kanta a cikin wannan lamari na aure, karshen lamarin ba zai yi mata kyawu ba da ma shi kansa mijin.
Abin da Manzon Allah (SAW) ya bayar da shawara shi ne, a auri namiji mai halaye guda biyu, na farko mai addini, na biyu kuma kyawun halaye. Ya kuma tsoratar akan fitina da fasadi mai girma da za su biyo baya idan ba haka aka yi ba. To yanzu ki dakatar da karatu daga nan, sai mu yi wata gasa a tsakanina da ke.
Da ni da ke duk mun yarda da cewar shawarar ma’aikin Allah ita ce mafificiya, kamar yadda muka yarda da cewar idan ba a bi maganarsa ba, nadama za ta biyo baya. To gasar ita ce, mu tambayi budurwa biyar wadda muka san cewa tana da wanda take so za ta aura, me ya sa take son ta aure shi? Idan budurwa uku daga cikin biyar din nan amsarsu ta dace da shawarar da ma’aikin Allah Ya bayar, shi ke nan na fadi, idan kuma an samu yin hannun riga, ni ne mai gaskiya a cikin wannan zance.
Zamanin dori, lokacin da mahaifa ke zaba wa ’yay’ansu abokan zaman aure, ba a cin karo da matsalolin aure da muke cin karo da su yanzu, kamar yawan sakin aure, cin amanar juna, rashin ganin mutuncin juna, dimbin zargi da dai sauran matsalolin aure. A fahimtata, mace ta zabo wa kanta mijin aure ba al’adar malam Bahaushe ba ce ta asali, daga baya aka kawo mana ita ta hanyar kallon fina-finan da ke dauke da al’adun wata al’umma daban. Don haka tun da kiyon bai karbe mu ba, mu yi hakuri mu bar shi. Mu bar ragamar aurenmu a hannayen iyayenmu.
Yabo da godiya sun tabbata ga Allah
Nasir Abbas Babi
08033186727