✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aure da zaman iyalin Kirista (10)

Har yanzu muna duba abubuwan da miji ko maigida ya kamata ya yi a cikin zaman gida tsakaninsa da matarsa da kuma yara idan Allah…

Har yanzu muna duba abubuwan da miji ko maigida ya kamata ya yi a cikin zaman gida tsakaninsa da matarsa da kuma yara idan Allah Ya ba su. Bari mu dubi wadansu kalmomin da aka yi amfani da su a wadansu ayoyi da muhimmancinsu, a cikin Littafin Afisawa:5:23, 25, 28–29: maganar Allah na cewa “Gama miji kai yake ga mace, kamar yadda Kiristi kuma yake kan ekklesiya ne, shi da kansa fa mai ceton jiki ne……”  “Ku mazaje ku kaunaci matanku, kamar yadda Kiristi kuma ya kaunaci ekklesiya, ya ba da kansa dominta….” “Haka nan ya kamata mazaje kuma su yi kaunar matansu kamar jikunansu. Wanda yake kaunar matarsa kansa yake kauna: gama babu mutum wanda ya taba kin jikinsa; amma yakan ciyar da shi yakan kiyaye shi, kamar yadda Kiristi kuma yakan yi da ekklesiya.” Kalmomin nan su ne: – kamar yadda, haka nan; wadannan kalmomin suna kwatanta mana dangantakar Yesu Kiristi da Ekklesiyarsa, yadda shi Yesu Kiristi yana lura da masu binsa, daidai kamar yadda Kiristi yakan lura da Ekklesiyarsa haka nan miji ya kamata ya lura da matarsa, dole ne ka ciyar da matarka, ka kuma kiyaye ta daga dukkan kowane hadari, eh har idan zai kai ga ba da ranka dominta, idan gaskiya kana kaunar matarka, ba zai zama da  wahala sosai ba ka ba da ranka dominta; idan har kana so ka zauna da matarka kamar yadda Ubangiji Yesu yana son ka yi, dole ne ka gane yadda shi Yesu yake tafiya da Ekklesiyarsa:
Kowane miji shi ne babban Priest na gidansa:
“Domin wannan fa ya wajabce shi ya kamantu ga ’yan uwansa a cikin dukkan abu, domin shi zama babban Priest mai jinkai, mai aminci, cikin matsaloli na wajen Allah, domin shi kaffarar zunuban jama’a. Gama yayin da shi da kansa ya sha wahala, ana jarabtarsa, yana da iko ya taimaki wadanda ake jarabtar su.” “Da shi ke fa muna da babban Priest mai girma, wanda ya ratsa sammai, Yesu dan Allah, bari mu rike shaidarmu. Gama ba mu da babban Priest wanda ba shi tabuwa da tarayyar kumamancinmu ba: amma wanda an jarabce shi a kowace fuska kamarmu, sai dai ban da zunubi.” “Gama kowane babban Priest, da shi ke kebabbe ne daga cikin mutane, sabili da mutane ake sanya shi cikin al’amuran da ke na Allah, domin shi mika baye-baye da hadayu domin zunubai: wanda ya iya hakura da jahilai da masu sabo, da shi ke shi da kansa kewayayye ne da kumamanci.” (Ibraniyawa: 2:17–18; 4:14–15; 5:1–2). Zaman miji ko maigida babban abu ne, kamar yadda Yesu Kiristi babban Priest mai jinkai mai aminci kuma, har da ya mai da kansa ba komai ba, ya kaskantar da kansa, ya dauki siffar mutum domin ya ji yadda mutum ke ji, ya kuma ji tausayin wadanda suka bar hanya; haka nan kowane magidanci mai bin Yesu ya kamata ya yi; shugabancin sanin Allah a cikin iyalinka ya rataya ne a wuyanka; wajibi ya zama cewa kowane miji ya nuna wa matarsa jinkai, ba ya zama kamar wani mutum wanda bai taba aikata laifi ba, mazaje da dama sukan nemi inda matarsu za ta yi dan kuskure kadan domin su samu su tsawata mata, abu na biye kuma shi ne ka zama mai aminci ga matarka, kada ka zama daya daga cikin mazaje masu ci amanar matansu. Kowane miji dole ne ya lura da lafiyar iyalinsa cikin jiki da ruhu.
Kowane miji mai ceton jikin ne:
“Gama miji kan mace yake, kamar yadda Kiristi kuma kan ekklesiya ne, shi da kansa fa mai ceton jiki ne” “Gama dan mutum ya zo gari neman abin da ya bace, ya cece shi kuma.” (Afisawa:5:23; Luka:19:10). Yesu Kiristi ya san ainihin dalilin da ya shigo wannan duniya, ya zo ne domin ya cece ta daga halaka, kai fa, wani irin shiri ne kake da shi domin matarka? Ceton da muke magana a kai; ba lallai ceto daga zunubi ko mutuwa ba, amma mai yiwuwa daga wadansu irin wahalhalu da take fuskanta, dole ne ka zama a wurin dominta.
Kowane miji shugaba ne mai mulkin gidansa:
Maganar Allah na koya mana cewa “Yesu ya kirawo su, ya ce masu, kun sani su wadanda an sanya su mallaki al’umma sukan nuna masu sarauta; manyansu kuma suna gwada masu iko. Amma ba haka yake a cikinku ba: amma dukkan wanda yake so ya zama babba a cikinku, bararku zai zama: kuma wanda yake so ya zama na fari a cikinku, bawan duka zai zama. Gama hakika dan mutum ya zo ba domin a yi masa bauta ba, amma domin ya bauta wa wadansu, ya ba da ransa kuma abin fansar mutane da yawa.” (Markus:10: 42– 45) “Sa’adda ya wanke sawayensu fa, da tufafinsa, ya zauna kuma, sai ya ce musu, kun san abin da na yi muku? Kuna ce da ni Malami da Ubangiji: kuna fadi daidai kuma; gama haka ni ke. Idan fa ni Ubangiji da Malami, na wanke sawayenku, ya kamata ku kuma ku wanke na juna. Gama na yi maku kwatancin, domin ku kuma ku yi kamar yadda na yi maku.” (Yohanna:13:12–15). “Yana kuwa mulkin nasa gidan da kyau, ’ya’yansa suna cikin biyayya da hankali shimfide sarai, (amma idan mutum ya rasa yadda zai mallaki nasa gidan, kaka zai goyi ekklesiyar Allah?)” 1 Timothawus:3:4–5). “Haka nan kuma ku mazaje, ku zauna da matanku bisa ga sani, kuna ba da girma ga mace kamar ga wadda ta fi rashin karfi da kuma masu tarayyar gado na alherin rai: domin kada addu’oinku su hanu.” “Da yake lallai Ibrahim zai zama babban al’umma mai karfi, dukkan al’ummar duniya kuma za su samu albarka a cikinsa? Gama na sansance shi da nufin shi mai hukunta ’ya’yansa  da iyalinsa a bayansa, su kiyaye tafarkin Ubangiji , domin su yi adalci da shari’a; domin Ubangiji Ya kawo wa Ibrahim abin da ya ambata a kansa.”(Farawa:18:18–19).
A matsayinka na mai gida ka zama shugaba, kuma Allah Ya ba ka rikon ragamar mulkin gidan a hannunka; amma abi lura guda shi ne, irin wannan shugabancin ba kamar na mutane duniya ba ne ko kadan, shugabanin wannan duniya suna gwada wa mabiyansu iko ne, suna kuma nuna musu sarauta, ba haka yake ba idan za mu yi mulki bisa ga tafarkin Allah. Yesu ya koya mana cewa ‘dukkan wanda yake so ya zama babba a cikinku, bararku zai zama,’ dole ne ka ja gaba; ka kuma zama misali ga iyalinka. Ba kawai ka yi ta zamanka kana hutawa ko kana karanta jarida, ita kuwa tana ta aiki domin kana gani ba aikinka ba ne. Kowane shugaba nagari, yakan kaskantar da kansa ya yi abin da watakila ma al’adarsu ba ta yarda ya yi ba. Idan har mun ba da gaskiya ga Yesu Kiristi, al’ada daya ce kawai muke da ita- wato Maganar Allah. Misali idan kana son matarka ta zama mai kwazo sosai cikin addu’a ko binciken Littafi Mai tsarki, sai ka yi kokari ka zama mai addu’a da bincike.
Mu ci gaba da godiya ga Allah domin taimakonSa da muke gani a wannan kasa tamu. Bari Allah Ya tsare kowane dayanmu, amin.