Atletico Madrid ta dauko hanyar zama zakarar gasar La Liga ta bana bayan shafe shekaru bakwai ba tare da cin kofin ba.
Kungiyar ta tunkari cin kofin karo na 11 a tarihi, kuma nasararta za ta tabbata ne idan ta ci wasanni biyun da suka rage mata.
- An ceto mutum 52 da aka yi safararsu a Kano
- Yadda sauran masu sallar Tahajjud 10 da aka sace a Katsina suka kubuta
Wasanni biyu na gaba da ke tunkaro kungiyar su ne wanda za ta kara da Osasuna da Real Valladolid duk a cikin watan Mayun da muke ciki.
A yanzu kungiyar ta sake bayar da tazara tsakaninta da kungiyoyin Barcelona da Real Madrid da ke matakin na biyu da na uku wadanda suka shafe shekaru suna musayar lashe kofin a tsakaninsu.
Tazarar da kungiyar ta bayar na zuwa ne bayan nasarar da ta yi yayin haduwarta da Real Sociedad a ranar Laraba, inda tazarar da ke tsakaninta da Barcelona da ke mataki na biyu a teburin gasar ya zama maki hudu.