Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta lashe gasar La Liga bayan ta doke kungiyar Real Valladoid da ci biyu da daya.
Aminiya ta ruwaito kungiyoyin Atletico Madrid da Real Madrid ne suke sa ran lashe gasar.
- El-Rufai na ganin kamar ya fi kowa ilimi — ASUU
- An yi yunkurin kashe Limamin Masallacin Harami yana cikin huduba
Kafin wasannin na ranar Asabar, Atletico Madrid na da maki 83, ita kuma Real Madrid na da maki 81.
Sai dai bayan wasannin, Atletico Madrid ta tara maki 86, ita kuma Real Madrid ta samu maki 84 bayan ita ma ta doke Villarreal da ci biyu da daya.
Tun shekarar 2014 rabon Atletico Madrid da lashe gasar La Liga din.
A minti na 18 dan wasan gaban Valladoid ya zura kwallo a ragar Atletico Madrid, wanda hakan ya ta da hankalin magoya bayansu.
Sai dai a minti na 57 dan wasan Atletico Madrid, Correa ya farke sannan a minti 67 ya zura kwallo na biyu a ragar Valladoid.
Suarez, wanda ‘korarren’ Barcelona ne ya taimakawa Atletico Madrid a wasanni biyu na kungiyar da suka gabata.
Kungiyoyin da suka lashe gasar Laliga daga kakar 2015 zuwa bana su ne:
2015: Barcelona
2016: Barcelona
2017: Real Madrid
2018: Barcelona
2019: Barcelona
2020: Real Madrid
2021: Atletico Madrid