Atletico Madrid ta samu nasarar lallasa Barcelona a wasan mako na takwas na gasar La Liga ta bana da suka fafata da yammacin ranar Asabar.
Atletico ta doke Barcelona da ci 2-0 yayin karawar ta gudana a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid mai daukar fiye da ‘yan kwallo dubu 68.
- Bashin N100bn: APC ta zargi Finitiri da wawure kudin jama’a
- Shafin Trust Plus: Gayyata ta musamman ga masu bibiyarmu
Dan wasa Thomas Lemar ne ya fara zura kwallo a minti na 22 da fara wasan, sai kuma daga bisani tsohon dan wasan Barcelona, Luis Suarez ya jefa wa Atletico kwallo ta biyu a minti na 43, dab da tafiya hutun rabin lokaci.
Wannan nasara da Atletico ta samu ta bata damar komawa mataki na biyu a saman teburin La Liga da maki 17 cikin wasanni takwas a gasar ta shekarar 2021/2022.
A halin yanzu dai dama na ci gaba subucewa Barcelona a karkashin jagorancin Ronald Koeman, wanda rashin tabbas ya dabaibaye makomarsa yayin da kungiyar ta shiga laluben wanda zai maye gurbinsa saboda rashin yi mata katabus.