Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa Dokta Umar Ardo ya ce tsohon Mataimakin Shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar ya koma jam’iyyar ne domin ya haddasa husuma a cikinta.
Dokta Umar Ardo, wanda daya ne daga cikin wakilai masu zabe da za su wakilci karamar Hukumar Jada da tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya fito a babban taron jam’iyyar da za a gudanar gobe ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC.
Dokta Ardo ya ce “Atiku Abubakar bai dawo PDP bisa gaskiya ba, bai dawo bisa tsarin mulki ba, bai dawo bisa kan doka ba. Kuma ya dawo ne saboda bukatun kansa… domin ya kawo rigima.”
Ya ce duk da yake Atiku Abubakar da magoya bayansa za su kara wa Jam’iyyar PDP karfi “Amma kuma akasari za su kawo wa jam’iyya ne rashin zaman lafiya saboda jama’arsa za su so taimaka masa wajen biyan bukatun kansa.”
Jigon na PDP ya ce tsohon Mataimakin Shugaban kasar ba zai iya kwace ikon jam’iyyar daga hannunsu ba, sai dai ya ce “Zai kawo tangarda da fadace-fadace da tashin hankali,” lamarin da zai yi tarnaki ga ci gaban jam’iyyar.
A ranar Lahadi ce Atiku Abubakar ya bayyana komawarsa Jam’iyyar PDP a shafinsa na Facebook, bayan ya zargi Jam’iyyar APC da kin cika alkawuran da ta yi wa jama’ar kasar nan, inda ya ce: “Gwamnatin APC ta yi alkawarin samar wa mutum miliyan uku aiki a kowace shekara amma mutum miliyan ukun ne suka rasa aikinsu a lokacinta.”
Atiku bai fito fili ya bayyana niyyarsa ta sake neman Shugabancin kasar nan ba a zaben shekarar 2019. Ya ce ya koma PDP ce saboda matsalolin da suka sa ya fice daga cikinta a shekarar 2014, “an warware su yanzu.”
Gwamnatin Buhari ba ta mayar da martani kan zargin na Atiku ba, amma Jam’iyyar APC ta ce koma ya fito takara a zabe mai zuwa Buhari zai kayar da shi.
A bangaren, Jam’iyyar PDP ta bakin shugaban rikonta, Sanata Ahmed Makarfi ta ce tana murna da komawar Alhaji Atiku cikinta, sai dai ta ce babu tabbacin za ta ba shi tikitin yin takara a karkashinta a zaben 2019 sai ya cika sharuddanta.