✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Atiku ya taya Gwarzuwar Hikayata ta 2020 murna

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya taya Maryam Umar murnar zama Gwarzuwar Hikayata ta bana. Atiku ya taya matashiyar murna ce cikin wani…

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya taya Maryam Umar murnar zama Gwarzuwar Hikayata ta bana.

Atiku ya taya matashiyar murna ce cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.

Kazalika tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya jinjina wa BBC Hausa kan bin da ya kira ‘kirkiro da wani tsari na karfafa wa ’ya’ya mata.’

Ya ce: “Ina taya Maryam Umar murnar samun wannan lambar yabo kuma nasararta ta nuna irin tarin yalwar ilimin da ake da shi a fadin kasar nan.”

“Ina kuma yaba wa sashen Hausa na BBC da suka kirkiro wannan tsari wanda zai ba ’ya’ya mata dama ta nuna hazakarsu da kuma karfafa musu.”

Maryam Umar mai shekaru 20 ’yar asalin jihar Sakkwato, ita ce gwarzuwar gasar gajerun kagaggun labarai ta BBC Hausa wato Hikayata a bana.

Maryam Umar

Labarin “Rai da Cuta” wanda Maryam Umar ta rubuta shi ne ya zama zakara a gasar ta shekara-shekara.

Maryam Umar ta lashe gasar a bana wadda ta rubuta labarinta ne a kan Azima, wadda mijinta ya dawo daga tafiya tare da alamar cutar COVID-19 a tare da shi.

Duk da cewa matarsa na da tsohon ciki, ya ki killace kansa sannan ya ki yarda cewa alamar cutar ce a tare da shi.

Ganin haka ne Azima ta kulle shi a daki, amma ba a jima ba ta gano cewa mijin nata ya riga ya harbe ta da cutar.

Kamuwarta da cutar ta yi sanadiyyar abun da ke cikinta, ita ma ta shiga fadi-tashin tsira da ranta.

Marubuciyar labarin daliba ce a Tsangayar Karatun Shari’a ta Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato.

Aminiya ta ruwaito cewa an yi bikin karramar matan uku da suka yi zarra a gasar Hikayata ta 2020 a ranar Juma’a.

Surayya Zakari mai shekaru 25 ce ta zo ta biyu a gasar ta bana a sakamakon kagaggen labarin da ta rubuta mai taken “Numfashin Siyasata.”

Labari na uku kuma shi ne wanda wata matashiya ‘yar jihar Kano Rufaida Umar Ibrahim ta rubuta mai suna “Farar Kafa”.