Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta rage yawan jiragen da Fadar Shugaban ke amfani da su ta hanyar sayar da su.
Ya kuma shawarce ta da ta zaftare kasafin kudin bana da akalla kaso 25 cikin 100 duba da kalubalen tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta.
Atiku, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2019 ya ce hadamar shugabanni na barazana ga makomar ‘ya’yan da za a haifa nan gaba.
- Ko zan mutu sai na sayar da kamfanin NNPC in aka zabe ni – Atiku
- Zan ci gaba da kokarin kwato wa ‘yan Najeriya ‘yanci – Atiku
Ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta bakin ofishin yada labaransa ranar Talata, yana mai cewa babu hikima Najeriya ta ci gaba da ajiye jirage a fadar shugaban kasa fiye da yawan na kasashen da take ciyo bashi a hannunsu.
“Ba wai iya watanda muka yi da albarkatun da muke da su ba kawai, a’a har na ‘ya’yan da za mu haifa nan gaba ta hanyar gadar musu da basussukan da ba gaira ba dalili.
“Ina kira ga gwamnati da ta gaggauta sayar da jiragen fadar shugaban kasa ko za a samu saukin kudaden kula da su.
“A rage kashe kudade kan abubuwan da ba su zama dole ba, sannan a rage yawan tafiye-tafiyen jami’an gwamnati zuwa kasashen ketare.
“A zahirin gaskiya kamata ya yi a sayar da jiragen alabasshi a yi amfani da kudaden a wasu ayyukan da za su amfani kasa tare da duba yiwuwar rage kudaden tafiyar da gwamnati”, inji Atikun.
Ya shawarci gwamnatin da ta farka ta fahimci halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki ta hanyar dakatar da ciyo basukan da take yi, yana mai cewa bai kamata hadamar shugabannin yau ta cutar da zuri’ar da za a haifa gaba.
Rahotanni dai sun nuna cewa akwai akalla jirage 10 da fadar shugaban kasar ke amfani da su yanzu haka.